Home / Lafiya / Rashin Tsaftacaccen Ruwan Sha Yafi Kashe Yara Fiye Da Bindiga – UNICEF

Rashin Tsaftacaccen Ruwan Sha Yafi Kashe Yara Fiye Da Bindiga – UNICEF

A wani rahoto da kungiyar UNICEF ta fitar mai taken “water under Fire” yayi duba ne akan irin hatsarin da yara ke fuskanta a yakunan da suka yi fama da yake-yake.

Rahoton ya maida hankali akan yara yan kasa da shekara 15, da ke rayuwa a kasashe 16 da suka yi fama da Yaki kuma sun gano cewa yara na mutuwa sanadiyyar rashin tsaftacaccen ruwan sha fiye da harbin bindiga.

Kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen da rahoton yayi duba a kai, yakin Boko Haram ya samar da babban gibi a Arewa masu gabashin kasar inda abin yafi ta’azzara.

Muhammad Fall, wakilin UNICEF a Najeriya ya ce mutum miliyan uku da dubu dari shidda (3.6) ke da bukatan tsaftacaccen ruwan sha, da kyakyyawan muhalli, da tsaftar jiki. Yara kuma suna cikin hatsarin kamuwa da yunwa, da cututtuka kamar su Amai da gudawa, da typhoid, da kwalara, da shan Inna (Polio).

Bugu da Kari, yara mata zasu iya fuskantar fyafe, saboda fita wurare yawon nemo ruwa ko wurin ba haya. Bayan haka, akwai matsalar jinin al’ada wanda hakan ka iya hana su samun ingantaccen ilima idan har ba a yi musu tanandi a makarantu ba.

A arewa masu gabashin kasarnan, a shekarar 2017 mutum 5,365 ne suka kamu da cutar kwalara kuma mutum 61 sun rasa rayukansu. A shekarar 2018, mutum 12,643 ne suka kamu da cutar kuma mutum 175 ne suka rasa rayukansu.

Mafi yawancin mutanen suna zaune ne a sansanonin yan gudun hijira, yayin da wasu suka gudu wuraren da yaķin bai shafa ba wanda a lokuta da dama, wurare ne da suke da wahalar ganowa saboda nisan su da al’umma (hard to reach).

Babban daraktan UNICEF Henrietta Fore ta ce rayuwar yara na cikin barazana saboda zama a yankunan da yaki ya shafa kuma hakan yasa suke fuskantar hatsarin rashin tsaftacaccen ruwan sha. A zahiri rashin tsaftacaccen ruwan sha yafi sanadin salwantar rayuwarsu fiye da harsashin bindiga.

About Amina Hamisu Isa

Check Also

Yin ƙarin gashin idanu hatsari ne ga lafiyar ido

Animashaun ta ce gashin ido na asali yana kare idanu daga tarkace, ƙura da ƙananan ƙwayoyin cuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *