PDP na buƙatar a soke zaɓen gwamnan Kano

72


Jam’iyyar PDP a jihar Kano ta yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ta soke zaɓen gwamna da ake ci gaba da gudanarwa a jihar a halin yanzu.


Da yake yi wa manema labarai jawabi ranar Asabar da rana, Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar, Alhaji Rabi’u Suleman Bichi ya yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki ta tanadi ‘yan daba a dukkan mazaɓu 208 da za a sake zaɓe a jihar don tayar da hankali.


A cewarsa, an hana wakilan jam’iyyar PDP shiga rumfunan zaɓe, kuma da yawa daga cikin su an doke su, an kuma kore su.


Mista Bichi ya bayyana zaɓen a matsayin wasan kwaikwayo.


Ya yi zargin cewa an shigo da ‘yan daba daga jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Plateau.


Ya ƙara da cewa ‘yan bangar siyasar suna zaɓe da katinan zaɓe da ba nasu ba ba tare da jin tsaro ba, wasu kuma suna nuna kansu a matsayin jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan