Ko kun san ya aka yi Ganduje ya ci zaɓe?

186


Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana Gwamna Jihar Kano mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kuma ɗan takara jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.


Da yake bayyana sakamakon zaɓen ranar Lahadi a Kano, Babban Baturen Tattara Sakamakon Zaɓe na Jihar, Farfesa Bello Shehu ya ce Gwamna Ganduje ya samu kuri’a 1,033, 695 inda ya doke Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’a 1,024,713.


“Cewa Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC, sakamakon cika ƙa’idojin doka, da samun ƙuri’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, kuma ya tabbata zaɓaɓɓe”, a cewar Farfesan.


Zaɓen gwamnan da aka sake ya nuna Gwamna Ganduje na jam’iyyar APC ya farfaɗo bisa ratar ƙuri’a 26,655 da Abba ya ba shi a zaɓen farko.


A zaɓen da aka sake ɗin dai, Ganduje ya samu kuri’a 45,876 inda Abba ya samu kuri’a 10,239.


Farfesa Shehu ya ce adadin masu rijistar zaɓe a Kano shi ne 5,426,989.


Ya ƙara da cewa adadin waɗanda aka tantance ya kai 2,269,305.


A cewar Farfesan, adadin ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen su ne 2,242,396, ya ce adadin ƙuri’un da suka lalace su ne 50,861.


Ratar dake tsakanin manyan ‘yan takarar biyu ita ce 9,210.


Adadin ƙuri’un da aka soke a zaɓen 9 ga watan Maris sun ka 128,324. Hakan ne yasa INEC ta ce dole a sake zaɓe a mazaɓu 207 dake ƙananan hukumomi 28.


Rahotanni sun tabbatar da cewa zaɓen na ranar Asabar cike yake da rikici-rikice a mazaɓu da dama, abinda yasa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi kira da a soke shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan