Nasarar Ganduje: Ko wane mataki Abba zai ɗauka?

44


Ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya ce zai tafi kotu don ya ƙalubalanci nasarar da Gwama Abdullahi Umar Ganduje ya samu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.


Wata sanarwa da mai magana da yawun Abba Kabir Yusuf, Sanusi Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin ta ce: “A fili yake cewa an ƙwace wa Kanawa abinda suke so ta hanyar yin amfani da hukumomin tsaro da wakilan INEC a matsayin masu bada dama”.


“Mun yanke shawarar ɗaukar matakin shari’a a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe ta hanyar tarin hujjoji da aka tattara, kuma idan Allah Ya yarda za a dawowa da Kanawa abinda suka zaɓa”, a cewar sanarwar.


Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A tarihin siyasar Kano, mun ga zaɓe mafi muni inda jam’iyyar APC mai mulki da Gwamnatin Jihar Kano suka yi amfani da dukkan matakai don tada fitina ga al’ummar Kano.


“Babu shakka, Kanawa sun shaida yadda maƙiya dimokuraɗiyya suka yi musu fashin abinda suke so da rana tsaka”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan