Wani Sanata ya bayyana buƙatarsa ta son zama Shugaban Majalisar Dattijai

35


Tsohon Jagoran Majalisar Dattijai kuma Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC, Mohammed Ali Ndume ya bayyana buƙatarsa ta zama Shugaban Majalisar Dattijai.


Sanatan ya bayyana haka ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 25 ga watan Maris, 2019, wadda ya aika wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Adams Oshimohole, ya kuma buƙaci jam’iyyar ta sa masa albarka gabanin ƙaddamar da Majalisar Dattijai ta 9.


Mista Ndume wanda ya yi imani cewa za a dawo da Shugabancin Majalisar Dattijai zuwa Arewa Maso Yamma inda ya fito, ya ce ya yanke hukuncin yin takarar ne sakamakon gogewarsa a harkar Majalisa da kuma burinsa na kai Najeriya zuwa mataki na gaba.


“Sakamakon gudanar da zaɓukan 2019 cikin nasara da gagarumar nasarar da babbar jam’iyyarmu ta APC ta samu a dukkan matakai, ina gabatar da wasiƙata ta buƙatar yin takarar Ofishin Shugaban Majalisar Dattijai a Majalisar Dattijai ta 9.


“Ina so in jaddada cewa na yanke shawarar fitowa takarar Shugaban Majalisar Dattijai ne saboda in bada gudunmawata wajen gina ƙasa”, in ji wasiƙar.


Mista Ndume, wanda ya taɓa zama Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai ta 6 da kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattijai ta 8 ya ce yana da dama da dukkan abinda ake buƙata don zama Shugaban Majalisar Dattijai don aiwatar da muradu da shirye-shiryen jam’iyyar APC.


A wasiƙar, Sanata Ndume wanda ya lura da cewa kiraye-kiraye daga manya-manyan ‘yan jam’iyyar APC daga Arewa Maso Gabas da sauran yankunan ƙasar nan sun ƙarfafa guiwarsa ya ce: “Bisa waɗannan dalilai da wasu da dama, ina so in gabatar da kaina don samun albarkar Jam’iyya, albarkar abokan aikina da ta ‘yan uwana ‘yan Najeriya don yin takarar muƙamin Shugaban Majalisar Dattijai.


Tsohon Jagoran Majalisar Dattijan ya bayyana cewa yana fatan “Jam’iyyar APC za ta ga hikimar da take cikin dawo da Shugabancin Majalisar Dattijai zuwa Arewa Maso Gabas duba da ƙoƙarinmu a zaɓukan 2019, kasancewar yankin ya ba Shugaban Ƙasa ƙuri’a ta biyu mafi yawa”.


Ya ce muƙamin zai ba shi damar biyan buƙatalun al’ummar Arewa Maso Gabas waɗanda rikicin tada ƙayar baya ya ɗaiɗaita, waɗanda suka samu rangwame sakamakon zuwan gwamnatin jam’iyyar APC a 2015.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan