Zaben Jihar Sokoto: Tambuwal Yayi Nasara

276

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwak ya samu nasarar lashe zaben jihar Sokoto.

Gwamnan wanda yayi takara a karo na biyu karkashin jam’iyyar PDP ya sha da kyar bayan da ya kada abokin adawarsa da kuri’u 342.

A zaben da aka kammala a ranar 23 ga watan maris, gwamna Aminu Waziri na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 512,002 yayin da takwaransa na jam’iyyar APC Ahmad Aliyu ya samu kuri’u dubu 511,660.

Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce zaben su bai kammalu ba, biyo bayan matsalolin da aka fuskanta a zaben na gwamnoni da aka yi a ranar tara ga watan maris.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan