Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC a jihar Bauchi ta bayyana Bala Mohammed, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a matsayin wadanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
INEC ta sanar da sakamakon zaɓen ne ranar Litinin da daddare bayan kammala tattara sakamakon zaɓen gwamna karo na biyu da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a mazaɓu 36 dake ƙananan hukumomi 15 da kuma na Ƙaramar Hukuma Tafawa Ɓalewa.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Litinin da misalin 11:18 na dare, Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen Jihar, Farfesa Mohammed Kyari ya ce Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 515,113 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, gwamna mai ci, Mohammad Abubakar, wanda ya samu kuri’a 500,625.
“Cewa Bala Mohammed na jam’iyyar PDP, sakamakon cika ƙa’idojin doka da kuma samun ƙuri’u mafiya yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe, kuma ya tabbata zaɓaɓɓe”, in ji Farfesa Kyari.
Hakan dai na nufin akwai tazarar kuri’a 14,488 tsakanin Bala Mohammed na jam’iyyar PDP da Gwamna Mohammed Abubakar na jam’iyyar APC.
‘Yan takara 31 ne suka yi takarar gwamna a jihar ta Bauchi.
‘Yan takarar sun haɗa da Ali Pate na jam’iyyar PRP, wanda ya samu kuri’a 46,326, sai Shu’aibu Ahmad na jam’iyyar NNPP wanda ya samu kuri’a 33,396, sai Mohammed Jumba na jam’iyyar GPN wanda ya samu kuri’a 23,000.
An dai sha taƙaddama a jihar ta Bauchi kafin INEC ta bayyana sakamakon zaɓen na ƙarshe sakamakon ɗumamar yanayin siyasa a jihar.