Kotu Ta Dakatar Da Yan Takarar APC A Jihar Zamfara

193

Wata kotun daukaka kara da ke jihar Sokoto ta ķi yarda da sakamakon fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulkin jihar Zamfara, tun daga kan gwamna har zuwa yan majalisun jihar.

A baya, jam’iyyar ta APC ta samu ruďani a lokacin da ta gudanar da zaben fidda gwani, wanda hakan ta kaisu ga zuwa kotu, kuma kotu ta yanke hukuncin korar dukkan yan takarar jam ‘iyyar a jihar Zamfara.

Gabanin zaben gwamnoni na ranar tara ga watan maris, wata kotu a jihar Zamfara ta yanke hukuncin amincewa da yan takarar jam’iyyar APC kuma ta yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa da ta sanya su a cikin zabe.

Bayan faruwar hakan, jam’iyyar APC ta samu damar shiga cikin zaben jihar kuma ta samu nasarar lashe zabukan.

Sai dai daya daga cikin sanatocin jihar, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana kin amincewarsa game da hukuncin da kotun ta yanke, domin a cewarsa basu da wani dalili na sake yanke wani hukunci daban da na farko.

Alkalin kotun na Sokoto ya ce kotun zata yanke hukunci mai tsauri domin hakan ya zama darasi ga sauran yan siyasar kasar nan.

A bangare guda, tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bukaci hukumar INEC da ta mika wa dan takarar jam ‘iyyar PDP shaidar zama gwamna. Sannan kuma ya taya dan takarar jam’iyyar PDP murnar lashe zaben jihar.

Bugu da kari, ya jinjina wa sanata Kabiru Marafa bisa namijin kokarinsa don hana magudi duk da cewa dan jam’iyyar APC ne.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan