Mintuna kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bauchi, Gwamman Jihar, Mohammed Abubakar ya karɓi faɗuwa ya kuma taya Bala Mohammed murna.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Ali Ali ya fitar, Gwamnan ya gode wa al’ummar jihar Bauchi bisa goyon bayan da suka ba shi, ya kuma roƙe su da su ba gwamnati mai zuwa irin wannan goyon baya.
“Ina taya ɗan uwana, Sanata Bala Mohammed murna bisa nasarar da ya samu a zaɓe”, in ji Gwamnan a wata sanarwa ta gaggawa.
“Na yi farin cikin lura da cewa duk da zafin yaƙin neman zaɓe a jiharmu, an samu nasarar gudanar da zaɓen na lumana ba tare da zubar da jini ba.
“Ina so in gayyaci sabon zaɓaɓɓen Gwamna da ya zo mu yi aiki don tabbatar da miƙa mulki cikin nasara.
“Babu shakka, na gode wa dukkan al’ummar jihar Bauchi sakamakon goyon bayan da suka ba gwamnatina, kuma ina riƙon su da su bada irin wannan goyon baya ga gwamnati mai jiran gado.
“Ina kuma kira ga zaɓaɓɓen Gwamna mai jiran gado da ya gargaɗi magoya bayansa su zama masu kiyaye doka yayin da suke murnar lashe zaɓen tun da lokacin yaƙin neman zaɓe ya wuce”, in ji Gwamna Abubakar.
A ranar Litinin ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC a jihar Bauchi ta bayyana Bala Mohammed, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a matsayin wadanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
INEC ta sanar da sakamakon zaɓen ne ranar Litinin da daddare bayan kammala tattara sakamakon zaɓen gwamna karo na biyu da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a mazaɓu 36 dake ƙananan hukumomi 15 da kuma na Ƙaramar Hukuma Tafawa Ɓalewa.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Litinin da misalin 11:18 na dare, Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen Jihar, Farfesa Mohammed Kyari ya ce Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 515,113 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, gwamna mai ci, Mohammad Abubakar, wanda ya samu kuri’a 500,625.
“Cewa Bala Mohammed na jam’iyyar PDP, sakamakon cika ƙa’idojin doka da kuma samun ƙuri’u mafiya yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe, kuma ya tabbata zaɓaɓɓe”, in ji Farfesa Kyari.
Hakan dai na nufin akwai tazarar kuri’a 14,488 tsakanin Bala Mohammed na jam’iyyar PDP da Gwamna Mohammed Abubakar na jam’iyyar APC.
‘Yan takara 31 ne suka yi takarar gwamna a jihar ta Bauchi.
‘Yan takarar sun haɗa da Ali Pate na jam’iyyar PRP, wanda ya samu kuri’a 46,326, sai Shu’aibu Ahmad na jam’iyyar NNPP wanda ya samu kuri’a 33,396, sai Mohammed Jumba na jam’iyyar GPN wanda ya samu kuri’a 23,000.