Sakamakon zaɓen gwamnan Kano: Jam’iyyun Hamayya sun bayyana matsayinsu

165

Jam’iyyun hamayya 42 a jihar Kano ƙarƙashin Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun Hamayya, CUPP sun yi watsi da sakamakon zaɓen gwamna karo na biyu da aka yi ranar 23 ga watan Maris a jihar.


Sun yi zargin cewa zaɓen cike yake da rashin bin ƙa’idoji.

Shugaban Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun Hamayyar na Jihar Kano, Mohammed Abdullahi Rahi ya sanar da wannan matsaya tasu lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi ranar Talata a jihar Kano.


Ya ce zaɓe gwamnan karo na biyu da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta gudanar cike yake da tashin hankali, aringizon ƙuri’u, tsoratarwa da kuma hana masu zaɓe kaɗa ƙuri’a.


A cewarsa, an samu rahotonnin bangar siyasa da tsoratar da masu zaɓe a kusan dukkan inda aka gudanar da zaɓen gwamnan zagaye na biyu, haɗi da rahotannin rasa rayuka, siyan ƙuri’a a fili da sauran laifukan zaɓe.


“A fili yake cewa tashin hankali da aka samu lokacin da aka gudanar da zaɓen 9 ga watan Maris wanda ya haifar da soke sakamakon wasu mazaɓu bai kai abinda muka gani ba lokacin zaɓen 23 ga watan Maris, duk da haka Hukumar Zaɓe ta yi burus da abubuwan da suka faru ta hanyar karɓa da sanar da sakamako.


“To a nan ne muke watsi da haramtacciyar sanarwa da aka bayar ta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon zaɓaɓɓen gwamna a zaɓen zagaye na biyu na ranar 23 ga watan Maris da aka kammala kwanan nan saboda rashin bin ƙa’ida da maguɗin zaɓe kafin, lokacin da bayan zaɓukan”, in ji Mista Rahi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan