INEC ta sa ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamna a Adamawa

197

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ayyana ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2019 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamna karo na biyu a jihar Adamawa.

Hukumar Zaɓen ta bayyana haka ne ranar Talata a shafinta na Twitter.


Ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne a ƙananan hukumomi 14 dake jihar inda ake da masu rijistar zaɓe 40,988.


A cewar INEC, masu zaɓe za su je mazaɓu 44 ne don su kaɗa ƙuri’unsu a ranar Alhamis ɗin daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana a yankunan rijista 29.


INEC ta sa wannan sabuwar ranar ne jim kaɗan bayan da wata Babbar Kotun Jihar Adamawa ta yi watsi da umarnin kotu da ya hana INEC ɗin gudanar da zaɓen gwamnan karo na biyu a mazaɓu 44 na jihar.


INEC ta kasa gudanar da zaɓen gwamnan karo na biyu ne a jihar sakamakon ƙara da ɗan takarar gwamna a jam’iyyar MRDD, Murtala Shaba ya shigar da ita.


Shaba ya maka INEC a kotu ne sakamakon ƙin sa alamar jam’iyyarsa ta MRDD a kan takardar zaɓe a zaɓen gwamna da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris.


A ranar 11 ga watan Maris, Babban Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen Jihar Adamawa, Farfesa Andrew Haruna ya bayyana zaɓen gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba yayin da yake sanar da sakamakon zaɓen a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe dake Yola, babban birnin jihar.


Ya bayyana cewa tazarar kuri’a 32,476 dake tsakanin ɗan takarar jam’iyyar PDP da na APC ba ta kai yawan ƙuri’u 40,988 da aka soke ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan