Kungiyar Amnesty International Ta Bayyana Matsayar Ta Akan Zaben Jihar Kano

284

Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin Tarayya da ta gudnar da bincike akan zargin da ake yi na tada hankula da yan daban siyasa suka yi, tare da cin zarafin ma’aikatan jarida , da masu zabe a lokacin zaben cike gurbi naa ranar Asabar 23 ga watan maris a jihar Kano.

Mai magana da yawun hukjmar Isa Sanusi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattauna wa da BBC Hausa, karkashin kulawar kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a garin Damaturu dake jihar Yobe.

Kungiyar ta yi Allah wadai da keta haddin dan Adam da aka yi musamman akan yan jarida da masu zabe a jihar Kano, a lokacin zaben cike gurbi.

Ya ce, an samu matsalolin tsaro a guraben zabe, inda mutane dauke da makamai sun razana tare da dakatar da zabe. Kuma jami’an tsaro basu kokarta ba wajen kare hakkin jama’a yanda ya kamata ba.

Hakan yasa wakilan kungiyar masu sa ido akan harkar zabe suka kasa karasawa mazabu don ganin yadda zaben ya gudana saboda rashin tsaro.

Kungiyar ta kara da cewa jami’an Yansanda da shugabannin jam’iyyu sun kasa dakatar da hare-hare akan jami’an zabe da sauran mutane daga yan daban siyasa da suke dauke da makamai a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa wanda ke dauke da kuri’u daya bisa uku a zaben cike gurbin na jihar Kano.

Kamfanin Dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa masu sa ido a harkar zabe na kungiyar European Union a ranar litinin 25 ga watan maris sun bayyana cewa an samu tashin hankali, da razanar da masu zabe a zabukan cike hurbi da aka gudanar a ranar asabar 23 ga watan nan a wasu bangaren jihohin Kano, da Benue, da Bauchi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan