Manyan Kalubalen Da Gwamna Ganduje Zai Fuskanta

193


Bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta kammala zaben jihar Kano aranar Asabar 23 ga watan maris, an bayyana sakamako a ranar lahadi kuma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasarar lashe zaben.

An fuskanci matsaloli da dama a zaben da aka yi na cike gubi a jihar Kano kuma hakan ya bar baya da ķura domin kuwa magoya bayan jam’iyyar PDP na ta ce-ce-ku-ce don suna zargin sake zaben wani shiri ne na jam’iyyar APC mai mulki na yin magudi ganin cewa jam’iyyar PDP ce ke kan gaba a zaben da aka gudanar na ranar tara ga watan maris.

Shafin BBC Hausa sunyi duba tare da yin nazari akan yadda mulkin gwamna Ganduje zai kasance da iri kalubalen da zai iya fuskanta.
Ga jerin matsalolin da zasu tunkaro gwamna Ganduje.

 1. Rarrabuwar kan al’umma a jihar.
  BBC Hausa sun rawaito tsokacin da mai sharhi akkan al’amuran siyasa, malama Kabiru Sa’idu Sufi yayi akan matsalolin, inda ya ce akwai rabuwan kai a cikin al’umma domin kuwa zaben ya nuna cewa mutane sun kasu kashi biyu kuma hakan ya hada da malaman addini, da yan siyasa da shugabannin al’umma. Don haka ya kamata a shawo kan al’umma a hada su wuri daya.
 2. Harkar Tsaro.
  An samu tashe-tashen hankula a lokacin zaben inda ake zargin cewa akwai wasu bangarori da ke hayar ýan daba don cimma bukatunsu. An samu yawaitar ýan daba rike da makamai da suke yima jama’a barazana, din haka akwai bukatar inganya tsaro a jihar.
 3. Harkar Ilimi.
  Jam’iyyar Adawa PDP ta yi amfani da harkar ilimi a yakin neman zabe don suna ganin gwamnatin Ganduje ba ta mai da hankali ba a wannan fannin. Jama’a da dama na ganin cewa fannin ilimi ya samu cibaya a yanzu idan aka kwatanta da gwamnatin baya. Don hakka, gwamnati tana bukatar mayar da hankali ga fannin.
 4. Inganta Rayuwar Al’umma.
  Sakamakon zaben cike gurbi ya nuna cewa mafi yawancin kuri’un da gwamna Ganduje ya samu daga karkara ne. Don haka ya kamata gwamnati ta yi musu ayyukan ingatan rayuwa domin kuwa akwai kauyuka da suke fama da rashin wutan lantarki, da ruwan sha da sauransu. Hakan ba yana nufin ya yi fatali da cikin gari ba, amma ya samu hanyar da zai kawo dai-daiton ayyuka a jihar.
 5. Mutanen da zai yi aiki da su.
  Dukkan kalubalen da gwamnan zai fuskanta sun ta’allaka ne kan irin mutanen da suke zagaye da shi. Don haka lokaci ya yi da gwamnan zai natsu ya yi nazari domin zabo aanda zasu taimaka masa a gudanar da mulki, ya karasa ayyukan da ya fara, sannan kuma ya dasa sababbi.

Daga karshe , BBC Hausa sun bawa gwamnan shawara da ya toshe kunnuwansa kuma ya rufe idanu, ya mayar da hankali wajen kawo cigaban da ya yi wa al’ummar Kano alkawari ganin cewa akwai adawa mai karfi a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan