A yau ne da sassafe shahararren malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano da masu garkuwa da mutane suka sace, Sheikh Ahmad Sulaiman ya samu ‘yanci shi da mutane biyar da aka yi garkuwa da su tare.
Da yake tabbatar da sakin nasu a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, Babban Jami’in Bataliya ta 17 ta Rundunar Sojojin Najeriya dake Katsina, Birgediya Janar Lukman Omoniyi ya ce waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin sun samu gwaje-gwajen lafiya da dama a Cibiyar Kula da Lafiya ta Bataliyar Sojin.
Ya ce Rundunar Sojin Najeriya a shirye take wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina da ma na ƙasa gaba ɗaya.
Kimanin kwanaki 13 da suka gabata ne ne masu garkuwa da mutane suka sace Sheikh Ahmad Sulaiman tare da wasu mutane biyar da suke tare da shi a hanyar Ƙanƙara zuwa Sheme yayin da suke dawowa daga jihar Kebbi.