‘Yan takarar da suka ci zaɓe a APC a Zamfara sun ga samu sun ga rashi

153

‘Yan takarar da suka lashe zaɓe a APC a jihar Zamfara sun ga samu sun ga rashi domin kuwa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bada sanarwar dakatar bada Takardun Shedar Cin Zaɓe ga sabon zaɓaɓɓen gwamna da sabbin zaɓaɓbun ‘yan Majalisun Dokokin Jihar da aka zaɓa a karkashin tutar jam’iyyar APC.


Wannan mataki na Hukumar Zaɓe ya biyo bayan wani umarni da Kotun Ɗaukaka Ƙara dake Sokoto ta bayar wanda ya yi watsi da hukuncin wata Babbar Kotun Jihar Zamfara da ya ba jam’iyyar APC damar tsayar da ‘yan takara a jihar.


“INEC ta samu hukuncin Kotun Ɗaukaka ta Sokoto game da tsayar da ‘yan takara da jam’iyyar APC ta yi a Zamfara kuma tana kan nazarin wannan hukunci.


“Sakamakon haka, an dakatar da bayar da Takardun Shedar Cin Zaɓe ga sabon zaɓaɓɓen Gwamna da sabbin zaɓaɓbun ‘yan Majalisun Dokoki da aka shirya farawa ranar Laraba, 27 ga watan Maris, 2019”, INEC ta wallafa haka a shafinta na Twitter.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan