Home / Gwamnati / Yadda rayuwata ta kasance a hannun masu garkuwa da mutane- Malam Ahmad Sulaiman

Yadda rayuwata ta kasance a hannun masu garkuwa da mutane- Malam Ahmad Sulaiman


Labarin da BBC Hausa ta wallafa na cewa fittacen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Alaramma Ahmed Suleiman ya bayyana irin ukubar da suka shiga a hannun masu satar mutane don kudin fansa.

An yi garkuwa da malamin ne a ranar 14 ga watan Maris kan hanyar ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina da ke Arewacin kasar.

Amma a ranar Alhamis 27 ga watan Maris, Rundunar Sojojin Najeriya ta ceto shi da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.


Rundunar Sojojin Najeriya sun ceto fitaccen malamin Ƙungiyar Izalan nan a Najeriya, Alaramma Ahmad Suleiman da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

Da yake jawabi a fadar Sarkin Katsina jim kadan bayan ceto shi, Malamin ya ce al’amarin mummunan abin tunawa ne “Sai dai Alhamdulillahi tun da Allah ya kwato mu,” in ji shi.


Ya ƙara da cewa: “Kullum su kan ce mana ai tun da yanzu aka ce hukuma ta shiga to Malam ba za ku koma gida ba, ko an kawo kuɗin nan sai mun kashe ku.

“Kullum ba abin da muke ji a kunnuwanmu sai kalmar za a kashe mu, sannan a yi ta harba bindiga a gabanmu. Gaskiyar magana kwanaki ne masu wahala sosai,’ in ji Malam Ahmad.

Malamin ya kuma ce: “Sai dai hakan jarrabawa ce kuma darasi ne. Ubangiji kan jarraba bawa don daga darajarsa ko yafe masa wasu zunubansa.

“Ina gode wa Allah da Rundunar Sojin Najeriya da kuma malamanmu na Ƙungiyar Izala.

“Haka muke taruwa ni da yaran mu yi ta kuka,” in ji Malam Ahmad.

Ya kuma ce sai da ya sauke Al-Kur’ani mai girma har sau shida a kwanakin da suka shafe hannun mutanen.


Sojojin sun bayyana cewa tun bayan garkuwa da malamin, Shugaban Hafsan Sojin Ƙasar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ba Runduna ta 17 ta Sojojin Ƙasar umarnin ceto malamin.

Sojojin sun ce sun yi amfani da dabaru iri-iri da suka haɗa da tattara bayanan sirri da kuma aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jam’ian tsaro wajen ceto malamin.

Sun bayyana cewa a yanzu haka malamin da sauran malaman da aka yi garkuwa da su na cikin koshin lafiya bayan likitocin sojojin sun duba lafiyarsu.

Har ya zuwa yanzu, babu wani ƙarin bayani kan ko an kama waɗanda suka yi garkuwa da malaman ko ba a kama su ba.

Martanin Ƙungiyar Izala


Ƙungiyar Izala ta kasa a Najeriya ta bayyana farin cikinta game da kubutar da Sheikh Ahmad Sulaiman da rundunar sojin kasar ta yi.

Sai dai bayanan da BBC ta samu ya nuna cewa ba a kama kowa daga cikin masu garkuwa da mutanen ba.

Wata majiya ta sojin ta shaida wa BBC cewa an gayyaci sojojin ne domin taimakawa wajen gano malamin, kuma a shirye suke su ci gaba da taimakwa domin ganin an shawo kan matsalar wadda ke addabar sassa daban-daban na kasar.

Kimanin makonni biyu da suka wuce ne aka kama Sheikh Ahmad Sulaiman yana kan hanyarsa ta komawa Kano, a wani yanki na jihar Katsina, kuma masu satar mutanen a baya suka nemi a biya su daruruwan miliyoyi kafin sakinsa.

Matsalar garkuwa da mutane dai ta taɗe tana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya a Najeriya.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *