Kaso 45 Na Yan Najeriya Zasu bar Kasar, Nan da Shekaru Biyar. Ko Kun San Dalili?

73

Sakamakon wani bincike da cibiyar gudanar da bincike na Pew Research Center da ke Kasar Amurka ta bayyana, sun gano cewa mafi yawan yan Najeriya na da burin barin kasar mu ta gado nan da shekaru biyar masu zuwa.

A rahoton da suka fitar a shafin yanar gizo na Fack Tank a jiya laraba 27 ga watan maris, sun bayyana cewa angudanar da binciken a shekarar 2018 a kasashe guda 12.

Sun kara da cewa, a kasashen Afrika, jama’a sun fi shirin yin hijira zuwa kasashen waje inda aka gano wasu har tanadin kudi suke yi, tare da yin bincike kan kasashen da suke da burin zuwa.

A kasarmu ta Najeriya da ta fi kowa yawan al’umma a nahiyar Afrika, kaso 45 ne na manya suke da niyyar barin kasar, nan da shekaru biyar. Watau kusan rabin mutanen da suka mallaki hankalinsu kuma kaso mafi girma da aka samu a cikin binciken.

Haka zalika, kaso 24 na manya a kasar Tunisiya sun kulla niyya irin na takwarorinsu yan Najeriya. Sai kasar kenya da ke biye musu, mai kaso 19 na nasu niyyar yin hijira.

A shekarar 2017, an samu manya masu niyyar yin hijira don yin cirani a kasashen duniya a kasar Senegal, da Ghana, da kuma South Afrika. Hakan na nuna yawaitar ķaruwan mutane da ke barin kasashen su da nufin cirani a nahiyar Afrika wacce ke fama da ķaruwan al’umma likin-balinkin.

Da rahoton yayi duba zuwa ga sauran kasashen duniya, kasar Philippines na da manya kaso 15 masu niyyar hijira zuwa kasashen waje duk da cewa kasar tana da tsohon tarihi na mutane masu yawon zuwa cirani.

Amma a kasar Indiya, an samu kaso biyu na manya masu niyyar hijira, da kaso takwas a kasar Brazil duk da cewa kasashen biyu sun fi kowacce kasa yawan yan cirani a duniya.

Binciken ya gano cewa mutane na gujewa kasashensu saboda wahalhalu da suke fuskanta na tsadar Rayuwa, da rashin ababen more rayuwa, da tashin hakula, da yake-yake da dai sauransu.

Kuma, mafi yawa daga cikin masu niyyar yin hijirar suna da burin zuwa kasashen waje. A kasar Tunisiya, kaso 68 daga cikin masu niyyar yin hijira, suna da burin zuwa kasashen Tarayyar Turai watau European Countries. A kasar Kenya kuwa, kaso 33 daga cikin yan hijirar suna da burin zuwa kasar Amurka, sai kaso 25 da ke burin zuwa wasu kasashen mu na Afrika. A Najeriya kuwa, kaso 28 daga ciki na da burin zuwa kasar Amurka, sai kaso 19 da ke burin zuwa kasakshen Tarayyar Turai, sai kaso 19 kuma masu burin zuwa kasashen Larabawa.

Binciken ya nuna cewa daga cikin yan kasashen Najeriya, da Tunisiya, da Kenya masu niyya, ba duka ne zasu samu damar cika burinsu ba. Amma mafi yawa daga cikin su na bibiyar matakai da zasu samu damar barin kasashen na su nan da wasu ýan shekaru.

Mutane daga Kasashen Najeriya, da Tunisiya, da Kenya masu rike da shaidar kammala karatu na Difiloma ko fiye da haka sun fi samun tabbacin tafiya. Kusan fiye da rabin mutanen da ke zaman cirani a kasashen Amurka da Ingila suna da shaidar karatu kuma mafi karanci a ciki shine shaidar kwalejin Ilimi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan