Sakamakon zaɓen gwamnan Kano: Jam’iyyun Hamayya sun yi amai sun lashe

31


Jam’iyyun Hamayya 42 a jihar Kano ƙarƙashin Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun Hamayya, CUPP sun bayyana goyon bayansu bisa nasar da Gwmna Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaɓen gwamna karo na biyuda aka gudanar makon da ya gabata.

Shugaban jam’iyyun da suke ƙarƙashin CUPP a jihar, Alhaji Abdullahi Nuhu wanda ya bayyana kaɗuwa lokacin da suka kai ziyarar taya murya ga Gwamna Ganduje, ya yi Allah-wadai da wani taron manema labarai da ake cewa an yi inda CUPP ɗin ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kanon.

Isah, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Bada Shawara Tsakanin Jam’iyyu, IPAC, ya ce jam’iyyun siyasar 42 sun gamsu da sakamakon zaɓen, kuma ba za su ƙalubalance shi a kotu ba.

“Mun kaɗu da muka karanta abinda taron manema labaran ya ƙunsa, wanda ya yi watsi da gaba ɗayan yadda zaɓen ya gudana, yadda hukumomin tsaro suka gudanar da aiki, yadda INEC ta gudanar da aiki da kuma abu mafi muni bada sanarwar ƙalubalantar sakamakon zaɓen.”

“Mu a CUPP da muke ƙunshe da wakilan jamiyyu 42 bisa haɗin gwiwa da Kwamitin Bada Shawara Tsakanin Jam’iyyu, IPAC mun nesanta kanmu daga wancan taron manema labara na kunya, kuma mun yi Allah-wadai da shi gaba ɗaya.

“Muna kuma bayyana rashin jin daɗinmu ga waɗanda suka shirya taron manema labaran sakamakon yin amfani da Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun don bayyana buƙatun kai ta yin amfani da CUPP”, in ji shi.

Ya ce Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun ta lura da yadda aka gudanar da zaɓen a Kano kuma ta yi imani da cewa zaɓen yana da sahihanci.

Isah ya ce haƙiƙa an samu ‘yan tashe-tashen hankula a wasu mazaɓu, amma a cewarsa hakan bai isa ya sa a soke zaɓen ba ko kuma a ƙalubalance shi a kotu.

Da yake jawabi tun da farko, Gwaman Ganduje ya yi mamakin me yasa jam’iyyar PDP ce kawai ba ta yadda da zaɓen ba, duk da cewa ba ita kaɗai ta shiga zaɓen ba.

Ya yi alƙawarin gudanar da gwamnati da za ta tafi da kowa da kowa, za ta haɗa kan kowa don ci gaban kowa.

“Za mu tafi da kowa da kowa ba tare da lura da bambancin siyasa ba don ciyar da jihar Kano gaba”, in ji Ganduje.

Idan dai za a iya tunawa, ranar Talatar da ta gabata ne wani shi ma da yace Shugaban CUPP ne ya yi taron manema labarai inda ya ce CUPP ta yi Allah-wadai da yadda akan gudanar da zaɓen gwamnan Kanon.

Jam’iyyun hamayya 42 a jihar Kano ƙarƙashin Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun Hamayya, CUPP sun yi watsi da sakamakon zaɓen gwamna karo na biyu da aka yi ranar 23 ga watan Maris a jihar.

Sun yi zargin cewa zaɓen cike yake da rashin bin ƙa’idoji.

Shugaban Gamayyar Haɗaɗdun Jam’iyyun Hamayyar na Jihar Kano, Mohammed Abdullahi Rahi ya sanar da wannan matsaya tasu lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi ranar Talata a jihar Kano.

Ya ce zaɓe gwamnan karo na biyu da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta gudanar cike yake da tashin hankali, aringizon ƙuri’u, tsoratarwa da kuma hana masu zaɓe kaɗa ƙuri’a.

A cewarsa, an samu rahotonnin bangar siyasa da tsoratar da masu zaɓe a kusan dukkan inda aka gudanar da zaɓen gwamnan zagaye na biyu, haɗi da rahotannin rasa rayuka, siyan ƙuri’a a fili da sauran laifukan zaɓe.

“A fili yake cewa tashin hankali da aka samu lokacin da aka gudanar da zaɓen 9 ga watan Maris wanda ya haifar da soke sakamakon wasu mazaɓu bai kai abinda muka gani ba lokacin zaɓen 23 ga watan Maris, duk da haka Hukumar Zaɓe ta yi burus da abubuwan da suka faru ta hanyar karɓa da sanar da sakamako.

“To a nan ne muke watsi da haramtacciyar sanarwa da aka bayar ta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon zaɓaɓɓen gwamna a zaɓen zagaye na biyu na ranar 23 ga watan Maris da aka kammala kwanan nan saboda rashin bin ƙa’ida da maguɗin zaɓe kafin, lokacin da bayan zaɓukan”, in ji Mista Rahi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan