A ranar Juma’a ne Kotun Ƙoli dake Abuja ta tabbatar da Donald Duke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar SDP.
Kotun Ƙolin dai ta tabbatar da hukuncin wata Kotun Ɗaukaka Ƙara ne da tuni dama ta tabbatar da Donald Duke ɗin a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ta SDP.
Alƙalai biyar ne suka yanke wannan hukunci waɗanda suka haɗa da Ejembi Eko, Kudirat Kekere, Aminu Sanusi, Paul Galumje da Uwani Aji.
Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta tabbatar da Mista Duke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar SDP a watan Janairu, bayan watsi da hukuncin wata Babbar Kotu dake Abuja wadda ta hana Mista Duke ɗin takara.
Lokacin da aka gudanar da zaɓen fitar da gwani ranar 6 ga watan Oktoba, 2018, Mista Duke ya samu kuri’a 812 inda ya doke abokin karawarsa, Farfesa Jerry Gana wanda ya samu kuri’a 611.
Sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen fitar da gwanin, sai Farfesa Gana ya garzaya wata Babbar Kotu dake Abuja inda ya buƙaci ta hana Mista Duke takara.
Ranar 14 ga watan Oktoba, 2018, Babbar Kotun ta bayyana Farfesa Gana a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwanin ɗan takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar ta SDP, shi kuma Mista Duke ya ɗaukaka ƙara ya kuma yi nasara a yanzu.