INEC ta bayyana sakamakon zaɓen gwamnan Adamawa

311

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Umar Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.


Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen Jihar, Farfesa Adrew Haruna ne ya bayyana sakamakon zaɓen ranar Alhamis da misalin ƙarfe 12:33 na dare.


Da yake bayyana sakamakon, Mista Haruna ya ce Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 376,552, inda ya doke Gwamna mai ci na jam’iyyar APC, Jibrilla Bondow wanda ya samu kuri’a 336,386.


“Cewa Umar Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP, sakamakon cika ƙa’idojin doka da samun ƙuri’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, kuma ya tabbata zaɓaɓɓe”, in ji Farfesa Haruna.


Sakamakon na nufin Mista Fintiri na jam’iyyar PDP ya ba Mista Bindow na jam’iyyar APC ratar ƙuri’a 40,166.


A cewar BBC, jam’iyyar ADC ce ta zo ta uku a zaɓen, inda ɗan takararta, Abdulaziz Murtala Nyako ya samu kuri’a 113,237.


Jihar Adamawa dai na daga cikin jihohin da INEC ta bayyana zaɓen gwamnasu a matsayin wanda bai kammala ba.


A zaɓen 9 ga watan Maris, an samu ratar ƙuri’a 32,476, tsakanin ɗan takarar APC da na PDP, adadin da bai kai yawan ƙuri’u 40,988 da aka soke ba, dalilin da ya INEC ta ce zaɓen bai kammala ba.


Jihar Adamawa ita ce jihar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.


‘Yan takara 29 ne dai suka tsaya takarar kujerar gwamnan jihar ta Adamawa.

Kazalika kafin ranar da Hukumar Zaɓen, INEC ta ware domin gudanar da zaben cike gibin da aka yi a ranar 23 ga watan Maris, Babbar Kotun Jihar Adamawa ta bayar da umarnin dakatar da gudanar da ƙarashen zaɓen gwamnan a jihar saboda ƙarar da dan takarar gwamna na jam’iyyar MRDD a jihar ya shigar inda ya bukaci kotu ta soke zaɓen da aka yi saboda rashin sanya alamar jam’iyyarsa a takardar zaɓen.

To sai dai kuma a ranar 26 ga watan Maris wata kotu a jihar ta Adamawa ta sauya matsayarta bisa umarnin da ta bayar na dakatar da kammala gwamna a jihar , inda ta bayar da damar kammala zaɓen.

Da wannan nasara jam’iyyar PDP dai ta yi nasarar kawar da gwamna mai ci Umar Jibrilla Bindow na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, kamar yadda BBC ta bayyana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan