Muhimman Abubuwan Dubawa Kafin Ba Yara Waya

213

A shekarun da suka wuce, yara masu karancin shekaru basu fiya ta’ammali da wayoyi ba domin a lokacin ana amfani ne da wayoyin tarho ne don yin kira ko amsawa waya.

Daga baya bayan nan, an samu bunkasar cigaba a fannin fasahar sadarwa, hakan yasa aka samu samfuri-samfuri na wayoyin zamani masu amfani da yanar gizo. Ba ana kadai abun ya tsaya ba, an samu bayyanar kafofin sadarwa da dama da suke biyan bukatu dabam-dabam.

Abin lura anan shi ne yadda yara masu kananan shekaru ke amfani da wayoyin zamani watau smartphones har da kafofin sadarwa ba tarr da sa idon wani babba ba.

Iyaye da dama suna damuwa akan hakan domin kuwa mafi yawan yara na amfani da wayoyin a bisa ka’ida ba, kuma hakan yana taimakawa wajen lalacewan tarbiya. Dalilai da dama kan sanya iyaye ba ýaýansu wayoyi, yayinda wasu sukan gwammace yaran su dauki nasu wayoyi suyi amfni da shi nawani lokaci.

Masu ruwa da tsaki a lamarin sun dade suna tattaunawa akan lamarin da kuma lokacin da yafi dacewa domin a ba yaro waya. Abin damuwa ana shi ne yadda yara ke amfani da waya don kallon fina-finan batsa, ko haduwa da yan iskan abokai, ko fadawa hannun bata gari ko yan damfara, koyan dabi’un banza da sunan gayu ko burgewa, ko kin maida hankali ga karatu da dai sauransu.

Idan har dalili yasa iyaye zasu ba ýaýansu waya, yana da kyau suyi duba ga wadannan muhimman abubuwa kafin kafin tanke hukuncin mallaka musu wayar.

  1. Yana da kyau sanin halin yaro wurin kula da daukan nauyin al’amuran da suke shafe shi. Shin yaro yana kula da kayansa yadda ya dace. Idan ya ce zai yi abu yana cika maganarsa, misali idan ya ce zai je wuri, zai je inda ya faďa kuma ya dawo akan lokaci? Yaro mai hankali da kula zai iya amfani da waya bisa ka’ida.
  2. Yaro ya zama mai adani da tattalin kayansa da na wanin sa. Idan yaro yana shashanci da ballagazar da kayansa, da na wani, akwai yiwuwar ya ballagazantar da wayan, ko kuma yayi sake ta fada hannun bata gari.
  3. Idan yaro yana bukatar wayar don a san inda yake da kuma yanayin da yake ciki, to iyaye su maida hankali akan hakan. Kar a bari muhimmancin wayar ta canza zuwa wani dalili dabam.
  4. Bayan duba akan dalilin zai sa a ba yaro waya, ya kamata iyaye su yi duba ga abubuwan da ka iya biyo baya idan yaro ya samu wayar kamar samun damar shiga yanar gizo, da shafukan sadarwa, da abubuwa na ķale-ķalen zamani (trends) da saurasu.
  5. Iyaye su jaddada wa yaro muhimancin yin amfani da waya bisa ka’ida kuma a lokacin da ya dace, wurin da ya dace. Sannan a tanadi wani horo da za a tsorata yaro da shi idan ya ki bin ķa’ida.
  6. Iyaaye su nuna wa yaro illar yawan amfani da waya ga lafiyar dan Adam. Yana da kyau a zaunar da yaro a fahimyar da shi amfanin waya da illolinta. Hakaz zai ba yaro damar amfani da hankalin shi da yin nazari a lokacin da yake amfani da waya kuma zai guji abin da yasan illa ne a gare shi.

A karshe, yana da kyai iyaye su dinga bibibyar al’amuran ýaýansu idan suna rike da waya, suna tuntubarsu lokaci zuwa lokaci tare da jansu a jiki don sanin halin da suke ciki saboda gudun yin tufka ana yi musu warwara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan