Buhari zai halarci bikin rantsar da Shugaban Senegal

143

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Babban Birnin Tarayya, Abuja zuwa Dakar, Babban Birnin Senegal don halartar bikin rantsar da Shugaban Senegal, Macky Sall wanda ya samu nasarar lashe zaɓe a karo na biyu.


Femi Adesina, mai ba Shugaba Buhari shawara kan kafafen watsa labarai wanda ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Litinin a Abuja ya ce Shugaban zai je Senegal ne bisa gayyatar da Shugaba Macky Sall ya yi masa.


A cewar sanarwar, Shugaba Muhammadu Buhari wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen ECOWAS zai kasance Babban Baƙo a wajen bikin da sauran shugabannin Afirka za su halarta wanda za a yi a Diamniadio Exhibition Centre ranar Talata.


Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamnan Bauchi, Mohammed Abubakar, na Kaduna, Nasir El-Rufa’i da na Nasarawa, Tanko Al-makura ne za su raka Shugaban.


Sauran waɗanda za su kasance tare da tawagar Shugaban sun haɗa da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Geoffrey Onyeama, mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Majo Janar Babagana Moguno (mai ritaya), Darakta Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa, Ambasada Ahmed Rufa’i da sauran manyan ƙusoshin gwamnati.


“Ana sa ran Shugaban Ƙasar zai dawo ƙasar nan idan an gama bukukuwan rantsarwar”, a cewar sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan