Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPC ya ce ba wani bambanci da yake nunawa a wajen ɗaukar aiki.
Ndu Ughamadu, Janar Manaja na Sashin Huɗda da Jama’a na Kamfanin ya bayyana haka yayin wata ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ranar Litinin a Abuja.
Ranar Lahadi ne Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS ta yi watsi da wasu ƙa’idoji da Kamfanin ya gindaya wajen ɗaukar mutane aiki, inda ta yi zargin cewa ƙa’idojin ba su yi daidai da muradun talakawa ba.
Ƙungiyar ta ba Kamfanin wa’adin sa’o’i 72 da ya janye ƙa’idojin da ta ce ba su yi daidai da muradun masu buƙatar a ɗauke su aiki ba.
Haka kuma, wani lauya mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi ya yi barazanar maka NNPC ɗin a kotu biyo bayan abinda ya kira “ƙa’idar ɗaukar aiki dake nuna bambanci”.
Ya lashi takobin garzayawa kotu don tabbatar da kare haƙƙin ‘yan Najeriya waɗanda sun cancanta amma an hana su aikin saboda dalilin shekaru.
“A’a, ba maganar nuna bambanci a ƙa’idojin. Idan akwai wani abu, ya kamata a yaba wa Kamfanin a yanzu da yake ƙoƙarin ɗaukar ma’aikata don rage yawan rashin aikin yi a ƙasar nan”, in ji Mista Ughamadu.
A cewar Janar Manajan, sai da aka yi tunani sosai kafin a gindaya waɗannan ƙa’doji.
Ya ce tsawon shekaru waɗannan ƙa’doji NNPC ke bi wajen ɗaukar aiki.
Ya ce an kasa ƙa’idojin zuwa ɓangarori huɗu waɗanda kowane ɗan Najeriya zai iya shiga.
“Akwai ɓangarori da dama, akwai ɓangarori huɗu, idan ba ka cika ƙa’idar wani ɓangaren ba, sai ka je ta gaba, idan ba ka cika ta biyun ba, sai ka tafi ta uku da sauransu.
“Ga horon da ake ba waɗanda suka gama karatu, mun sa matakin shekara 28, na biyu shekara 34, na uku 37 na ƙarshe kuma 40. Saboda haka, duk ɗan Najeriyar dake buƙatar aiki wanda ya faɗo cikin ɗaya daga cikin ɓangarori huɗun ya cancanta”, in ji Mista Ughamadu.
Ya ce abin kaico ne wasu mutane sun yi yunƙurin neman aiki ba su yi nasara ba sai kuma su ce ana nuna bambanci a wajen ɗaukar aikin.
Da yake tsokaci game da wa’adin sa’o’i 72 da Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa NANS ta bayar na su cire ƙa’idojin ko kuma su yi zanga-zanga, ya ce ya kamata mambobin NANS su mayar da hankali akan karatunsa su fita da kyawawan shedar karatu.
“Ya kamata NANS su ci jarabawarsu su kammala karatunsu da farko wanda bayan haka ne za su cancanci ɗauka aiki.
“Abinda ya kamata NANS su fuskanta yanzu shi ne su yi karatu tuƙuru, su kammala karatu su samu digiri mai kyau. Har yanzu ba su gama karatu ba, kuma suna maganar aikin yi”, in ji shi.
Kamfanin na NNPC ya buɗe shafinsa na Intanet na ɗaukar aiki daga 13 zuwa 26 ga watan Maris, kuma tuni ya fara fitar da sunayen waɗanda suka buƙaci ɗaukar aikin.