Dimukoraɗiyya da Ci Gaba

199


Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 (Rubutaccen saƙo kawai)

Kowace ƙasa a duniya burinta shi ne ya za a yi ta samu ci gaba, waɗanne hanyoyi za ta bi wurin cimma wannan ci gaba, me za ta yi, kuma me za ta dakatar?

Samun ci gaba na nufin samuwar sauyi (canji) daga wani yanayi da ake ciki zuwa wani yanayin.

A lokuta mabambanta, masana sukan yi musayar ra’ayi dangane da abin da ake nufi da samun ci gaba.

Wasu a ɓangarensu, sun tafi a kan cewa a haƙiƙanin gaskiya babu wani abu mai kama da samun ci gaba. Haka kuma a ɗaya bangaren, akwai masanan da suka tafi a kan cewa tabbas akwai ‘samuwar ci gaba’, kuma suna kallon wannan ci gaba ne ta fuskacin ‘tattalin arziki’. Ci gaba a wurinsu shi ne ƙasa ta iya bunƙasa harkokin Kimiyya da Fasaha, ta yadda tattalin arzikinta zai haɓɓaka. A fahimtar wadannan masanan, ba zai yiwu wata ƙasa wacce ba ta ci gaba ba, ta iya kai wa ga waɗancan abubuwa har sai ta kwaikwayi dukkan al’adun Yammacin Turai.

Ɓangaren masana na ƙarshe su ne waɗanda suka tafi a kan cewa idan ka ji ana yekuwar samun ci gaba, to babu ci gaban. Saboda su a fahimtarsu, a haƙiƙanin gaskiya ba ci gaba ake samu ba, face dai dogaro ga wasu da kuma wanzuwa cikin rashin ci gaba. Suna nufin cewa an gindaya sharadi ne da gangan cewa dole ne sai an kwaikwayi wasu ƙasashe sannan za a samu ci gaba, wanda kuma hakan ba zai taba faruwa ba a gaske.

Kamar misali, a lokacin da Najeriya ke ƙara ƙaimi wurin kwaikwayon abubuwa daga Amurka, babu ranar da za mu iya zama sak kamar Amurkan, wannan na nuna cewa babu ranar samun ci gaban.

Manufar Dimokuradiyya, shi ne ba wa al’umma ‘yanci, shi kuwa ‘yanci ba ya samuwa har sai an sami zaman lafiya a cikin al’umma. Zaman lafiya kuma yana haifar da ci gaban rayuwa, kuma yana inganta ƙasa da ruhin ɗan Adam.

Ƙasahen da suka samu ci gaba suna girmama tsarin Dimukoraɗiyya, girmama tsarin dimukuradiyya, shi ne ba wa al’umma damar zaɓen abinda suka zaɓa da kansu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan