An Kama Wasu Yan Najeriya Da Laifin Satar Kudi Har Naira Miliyan 200 A Daular Larabawa

191


An kama wasu yan Najeriya su biyar da laifin fashi da makami a hadaddiyar daular larabawa (UAE).

Barayin yan Najeriya sun saci kudi dirham miliyan biyu da dubu dari uku, wanda ya kai kimanin kudin Najeriya naira miliyan dari biyu wurin yan canji na sharjahof.

Matasan Barayin an bayyana sunayensu kamar haka; Emmanuel Ozo, da Benjamin Nwachukwu Ajah, da Kingsley Ikenna Ngoka, da Toochukwu Leonard Alusi, sai Chile Micah Ndunagu.

Rahoton Yansanda ya bayyana cewa matasan su hudu sun bankada wurin canjin tare da fasa gilasai da aka saka tsakanin masu saye da masu sayarwa sannan suka saci kudade yayin da daya ke mota yana jira fitowansu don tserewa.

A yayin da suke fashin, sun jiwa ma’aikata biyu wanda suka yi kokarin ja da su. Jami’an Yansanda sun kara da cewa yan fashin sun shigo kasar a ranar litinin 18 ga watan maris, da takardar ziyara na visa kuma sun dauki tsawon kwanaki biyu suna lura da wurin kafin su aikata fashin a tsakar dare, daf da lokacin rufewa a ranar laraba 20 ga watan maris shekarar 2019.

Yansanda sun iso wurin da lamarin ya faru mintuna bakwai da samun labarin kuma sun dauki duk wani bayanai da zai taimaka wajen kama barayin. Hakan ya taimaka musu wajen cafke daya daga cikin barayin a Sharjah.

Bayan ya shiga hannun, sai ya bada bayanin maboyan sauran inda aka kama guda biyu a Ajman, daya a Abu Dhabi sai dayan a Ras Al Khaimah. Yanzu haka Barayin sun amsa laifukansu kuma an mika su gaban shari’a domin fuskantar hukunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan