Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi suka ga shugaba buhari bisa salon mulkinsa musamman rawar da ya ke takawa ga arewacin kasarnan. Hakan ya nuna shugaba Buhari bai yi wa Arewa komai ba.
A wata hira da yayi da Mustafa Musa Kaita, BBC Hausa sun rawaito Bafarawa inda ya ce babbar matsalar da kasarnan ke fuskanta shi ne rashin tsaro, musamman garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa ana nuna bangaranci wajen gudanar da ayyukan cigaba a kasarnan. Sannan kuma ya yi kira ga shugaba Buhari da ya bude kunnuwansa ya saurari shawarwari da zasu iya kaiwa ga cigaba a kasa.
Attahiru Bafarawa ya yi wadannan kalamai bayan da shugaba Buhari ya lashe zabe a karo na biyu. Tattalin arziki, da cin hanci da rashawa, da tsaro sune abubuwan da shugaban ya bayyana ya sa a gaba domin kawo cigaba a kasar.