Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar ta-ɓaci a jihar

15

A ranar Laraba ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar taƙaita zirga-zirga ga matuƙa baburan gida da na haya a dukkan ƙananan hukumomi 14 dake jihar daga ƙarfe 7 na safe zuwa ƙarfe 7 na yamma.

Kwamishinan Kula da Ƙananan Hukumomi na Jihar, Bello Dankande Gamji ya bayyana wannan mataki a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa kafa dokar ta ɓacin ya zama wajibi duba da matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Kwamishinan ya kuma yi alhinin yadda aka yi garkuwa da wata mata a jihar tare da ɗanta kwanan nan lokacin da ta hau babur mai ƙafa uku don ya kai ta gida.

Kwamishinan, wanda Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Celestine Okoye ke kusa da shi lokacin da yake jawabi, ya ce za a baza jami’an ‘yan sanda a dukkan lungu da saƙo na birnin jihar don kama tare da hukunta masu kunnen ƙashi.

Ya kuma ƙara bayyana cewa da yawa daga cikin laifukan da ake aikatawa ana aikata su ne tare da haɗin bakin matuƙa babura tare da masu hawa.

“Mun san cewa za a ga wannan hukunci ya yi tsanani ko tsauri a kan al’ummarmu, to amma ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi don a kare al’ummarmu, a kare rayuka da dukiyoyi, a tabbatar da cewa zaman lafiya ya ɗore a dukkan faɗin jiharmu”, in ji Kwamishinan.

Jihar Zamfara dai ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da garkuwa da mutane, ƙona ƙauyuka da kisan mutane ba gaira ba dalili.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan