INEC na ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Rivers

67

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC na ci gaba ta tattara sakamakon zaɓen gwamna da na ‘yan Majalisun Dokokin Jiha a jihar Rivers biyo bayan dakatar da hakan ranar 10 ga watan Maris.

Sakamakon zaɓen da aka fitar kawo yanzu ya nuna jam’iyyar PDP ta lashe ƙananan hukumomi 13 daga cikin 15 aka tattara sakamakonsu.

Hukumar Zaɓen dai ta yi zargin cewa wasu mutane ne sanye da kayan soji suka tada fitina yayin tattara sakamakon zaɓen, inda bayan haka ne ta kafa wani kwamiti don yin bincike.

Bayan nan ne sai INEC ta fitar da sanarwa dake cewa za ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen daga 2 zuwa 5 ga watan Afrilu a ƙananan hukumomi 17 dake jihar.

Ƙananan hukumomin da jam’iyyar PDP ta ci sun haɗa da Port Harcourt City, Ikwere, Andoni, Eleme, Opobo Nkoro da Bonny.

Jam’iyyar ta kuma yi nasara a Okrika, Omuma, Tai, Ahoada East, Emoha, Etche, Ogba/Egbema/ Onelga.

Babbar jam’iyyar hamayya a jihar, AAC ta yi nasara a ƙananan hukumomin Akuku Toru da Oyibo.

Sakamakon zaɓen da INEC ta fitar zuwa yanzu ya nuna jam’iyyar PDP tana da ƙuri’a 426,279, yayin da jam’iyyar AAC ta samu ƙuri’a 129,855.

Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen Jihar, Teddy Adias ya ce a ranar Laraba da ƙarfe 10 na safe ne za a ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen da ya rage.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan