Ko kun san yaushe Maryam Abacha American University za ta fara aiki a Najeriya?

233


Gabanin ƙaddamar da ita a hukumance don fara aiki a Najeriya, Maryam Abacha American University ta naɗa Muhammed Magaji a matsayin Muƙaddashin Shugaban Jami’ar.

A wannan shekarar ne Jami’ar za ta fara aiki a muhallinta na din-din-din dake jihar Kano.

Tuni dama Maryam Abacha American University dake Maradi, Jamhoriyar Nijar ta fara bada karatu.

Sanarwar naɗin na Mista Magaji tana ƙunshe ne a wata sanarwa da Mamallakin Jami’ar, Adamu Gwarzo ya sanya wa hannu.

Wasiƙar ta ce an yi amfani da shawara da kuma sahalewar da kwamitin da aka ɗorawa alhakin nemo wanda za a ba wannan muƙami da kuma Hukumar Gudanarwar Jami’ar suka bayar.

A cewar Mista Gwarzo, naɗin ya fara aiki ne tun ranar 18 ga watan Maris.

Har lokacin naɗin nasa, Mista Magaji shi ne Shugaban Makaranta Ilimi Mai Zurfi dake Maryam Abacha American University, Maradi, Nijar.

Da yake tattaunawa da jaridar PREMIUM TIMES, Mista Gwarzo ya ce Maryam Abacha American University ta Najeriya za ta fara karatu a shekara ta 2019 a matsayin jami’a mai zaman kanta.

“Komai yana kan tsari, kuma Jami’ar za ta rika bada Shaidar Karatun Digiri a Likitanci, Kwasakwasan da ba su shafi Kimiyya ba da kuma Kimiyyar Zamantakewa.

“Haka kuma, Makarantar Nazarin Fasahar Lafiya dake Kaduna za ta fara aiki nan da wata ɗaya ko biyu. Komai ya kusa kammala”, in ji Mista Gwarzo.

Maryam Abacha American University ita ce jami’a ta farko mai amfani da harshen Turanci a ƙasar da ke amfani da harshen Faransanci, Nijar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan