Shugaba Buhari Ya maida Martani Ga Bafarawa

174

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya mayar da martani kan sukan da tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa yayi masa akan salon gudanar da mulkinsa.

Mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a madadin shugaba Buhari a wani hira da yayi da Mustapha Musa Kaita ta wayar tarho.

BBC Hausa sun rawaito cewa malam Garba Shehu ya kara da cewa Bafarawa bai yiwa shugaba Buhari adalci ba bisa kalaman da ya furta, inda ya kira ga Bafarawa da ya je ya tambayi jama‘ar jihohin Kaduna, da Adamawa, da Borno bisa kokarin da shugaban yayi musu akan harkar tsaro.

Bugu da kari, ya ce matsalokin tsaro da ke faruwa a hanyar Kaduna, da Birnin Gwari, da Zamfara da sauran wurare suna damun gwamnati kuma yanzu haka tuni shugaban kasa ya bawa sojojin sama da na kasa umarnin zuwa yankunan don magance abubuwan da ke damun jama’ar yankin.

Garba Shehu ya musanta duk wani zargi da suka da tsohon gwamnan yayi akan shugaba Buhari, kuma wannan martani ga Bafarawa ya zo ne a dai-dai lokacin da ake fama da rashin tsaro a wasu sassan arewacin kasarnan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan