Wata ‘yar Majalisa a Gombe ta ga samu ta ga rashi

156

Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zaman ta a Jos, babban birnin jihar Plateau ta soke zaɓen Rabi Daniel, ‘yar Majalisar Dokokin Jiha da aka zaɓa ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP mai wakiltar Billiri ta Gabas dake Jihar Gombe.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ta ba Rambi Iyalah Takardar Shaidar Cin Zaɓe a matsayin wanda aka zaɓa.

Rahotanni sun ce Mista Iyalah ya kayar da Misis Daniel a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar ranar 4 ga watan Oktoba, 2018.

Rahotanni sun ce Mista Iyalah ya samu kuri’a 25 inda Misis Daniel ta samu ƙuri’a 24 a zaɓen fitar da gwanin.

Bayan nan ne sai Jacob Lawal, wani lauya kuma Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen fitar da gwanin da Mista Magaji Lafiaji, Shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓen Fitar da Gwani na Jam’iyyar PDP a Jihar suka bayyana Misis Daniel a matsayin wadda ta lashe zaɓen fitar da gwanin.

Sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen, sai Mista Iyalah ya rubuta ƙorafi zuwa ga Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na Jam’iyyar, amma ya ce aka yi watsi da ƙorafin nasa.

Zargin cewa Kwamitin Ɗaukaka Ƙarar ya kasa yin adalci ne yasa Mista Iyalah ya garzaya wata Babbar Kotun Tarayya dake Gombe ranar 9 ga watan Janairu don neman a yi masa adalci.

Mista Iyalah ya roƙi Kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwanin, bisa dalilin cewa ya lashe zaɓen da ƙuri’a ɗaya, amma an yi masa maguɗi ne.

Kotun, ba tare da ji daga Misis Daniel ba, wadda ake ƙara ta farko sai ta yi watsi da ƙarar bisa dalilin cewa ba a bi ƙa’ida ba, ta kuma tabbatar da zaɓen ta a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar PDP, abinda ya tilasta Mista Iyalah garzayawa Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Da yake yanke hukunci ranar Alhamis a Jos, Mai Shari’a M.N Oniyangi ya yi watsi da wancan hukunci na Babbar Kotun Tarayya, inda ya ce alƙalin bai yi wa ƙarar adalci ba.

A cewar Mai Shari’a Oniyangi, hujjojin da wanda ya ɗaukaka ƙara ya gabatar sun nuna cewa tabbas shi ya ci zaɓen, amma an yi masa maguɗi ne.

“Bisa wannan shari’a da ake sauraro, ina so in yi watsi da hukuncin alƙalin Babbar Kotun Tarayya, in kuma bayyana cewa Mista Rambi Iyalah, wadda ya ɗaukaka ƙara shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na PDP da aka gudanar ranar 4 ga watan Oktoba, 2018”, in ji Mista Oniyangi.

Mai Shari’a Oniyangi ya kuma umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe da ya kama tare da bincikar Mista Lawal da Mista Lafiagi sakamon yin ƙarfa-ƙarfa wajen canza abinda mutane suke so.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan