Ko wane hali waɗanda suka yi garkuwa da Alaramma Ahmad Sulaiman ke ciki?

73

Jami’an tsaro sun cafke shahararren mai garkuwa da mutanen nan, Lawal Abubakar da mambobin ƙungiyarsa waɗanda suka yi garkuwa da Alaramma Ahmad Sulaiman da wasu mutane biyar a jihar Katsina lokacin da suka yi yunƙurin arcewa daga maɓoyar tasu.

A wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta na zamani, an ga shugaban ƙungiyar tasu yana cewa mambobin ƙungiyar sun riƙa kashe kansu da kansu jim kaɗan bayan sakin Aramma Ahmad.

Ibrahim, wanda mutum ne mai matsakaicin shekaru da wani abokin aikata laifin nasa wanda ya ce sunansa Iliya ya ce su goma ne suka sace Alaramma Ahmad.

Ibrahim ya ce bai taɓa haɗuwa ko ganin wani da ake kira Alhaji Dogo Nalade a fili ba wanda ya yi iƙirarin cewa shi ne shugabansu, ya ce amma sun riƙa yin waya da shi daga wani ɓoyayyen waje.

Shahararren mai garkuwa da mutanen ya ce an kama su ne lokacin da suke yunƙurin arcewa zuwa Obajana dake jihar Kogi don yin aikin ƙarfi bayan yin watsi da mummunar sana’arsu ta garkuwa da mutane.

Ya ce waɗansu mutane ne ke kawo musu makaman da suke yin amfani da su a wannan mummunar sana’a tasu, bayan nan kuma sai su buƙaci su ba su lada.

“Sakin Malam abu ne da ya ɗaure mana kai. Dalili kuwa shi ne duk da amincewa da muka yi gaba ɗaya cewa za mu karɓi kuɗi daga mutanensa da abokansa, daga baya kawai sai muka yanke shawarar mu bar shi ya tafi.

“Amma yaƙi ya ɓarke tsakanin mambobin ƙungiyarmu. Wasu abokan aikinmu sun kashe ‘yan ƙungiyarmu su biyu a daji. Koda yake dai biyu daga cikinmu da aka kama mun yi sa’ar tserewa daga dajin don kar a kashe mu, mambobinmu da suka fusata sun harbe mambobi bakwai har lahira”, in ji Ibrahim.

Alaramma Ahmad ya samu ‘yanci shi da mutane biyar ɗin da aka yi garkuwa da su tare ranar Alhamis, 27 ga watan Maris, 2019 bayan sun shafe kimanin mako biyu a hannun masu garkuwa da mutanen.

An sace malamin ne da sauran mutane biyar da suke tare da shi a hanyar Sheme zuwa Ƙanƙara dake jihar Katsina kan hanyarsu ta dawowa Kano bayan halartar wani taron wa’azi a jihar Kebbi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan