Miyatti Allah: Fulani Basu Da Hannu A Kashe-Kashen Jihar Zamfara

185

Kungiyar Miyatti Allah reshen jihar Zamfara tayi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da cewa jama’ar Fulani sun sami ilimi yadda ya kamata domin kawo karshen hare-hare da sace-sacen mutane a jihar.
Shugaban kungiyar Malam Ibrahim Sulaiman ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis 4 ga watan Afrilu a garin Gusau yayin da suke taron masu ruwa da tsaki a kan tsaro.
Malam Ibrahim yace samar da ilimi mai inganci a jihar musamman ga Fulani shi zai kawo karshen matsalar tsaro a jihar, don haka suke kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen tabbatar da cewa an samu ingantaccen ilimi a jihar.
Ya kara da cewa mafi yawa daga cikin jama’ar Fulani basu iya karatu da rubutu ba ballantana su san dokar kasa har su bita yadda ya kamata. Hakan yasa suke rokon gwamnati da ta rike fannin ilimi hannu bibbiyu.
Shugaban ya karyata ikirarin da ake yi na cewa Fulani sune ke aikata miyagun ayyukan da ke faruwa a jihar, sannan kuma ya yi kira ga gwamnati da ta gudanar da kwakkwaran bincike akan lamarin.
Daga karshe ya karyata zargin da ake yi na cewa akwai sabani a tsakanin Fulani da Hausawa a jihar, kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da aikinsu ba tare da tsoro ko alfarma ba don kama masu laifi. Sannan ya yi kira ga al’ummar Fulani da su kasance masu zaman lafiya da bin doka, kuma kar su sake su dauki doka a hannunsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan