Rundunar Yansanda ta jihar Zamfara ta karyata rahoton gidan wani jarida da yace rundunar ta sa dokar hana fita a jihar biyo bayan yawan kashe-kashe da garkuwa da mutane domin biyan kudin fansa.
A wani hira na musamman da jaridar Daily Post a jihar Gusau, mai magana da yawun rundunar S.P. Muhammad Shehu yace mai rahoton bai fahimci rundunar Yansandan ba shi yasa ya yi rahoton ba dai-dai ba.
S.P. Muhammad yace , rundunar Yansanda ta hana baburan Acaba da Adaidaita sahu watau Keke-Napep zirga -zirga daga karfe shida na yamma zuwa bakwai na safe a kullum saboda sun gano yan-ta’addan na amfani da wadannan ababen hawan wajen kaddamar da mugun aikinsu.
Ya kara da cewa rundunar Yansanda bata sanya dokar hana zirga-zirga ba a jihar ta Zamfara ba, dan jaridar ne ya yi rahoton ba dai-dai ba.
A ranar Laraba da ta gabata ne, kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun gargajiya ya yi taron ganawa da Sarakuna da shugabannin Fulani a garin Gusau, inda yace gwamnati tana kan bakanta na dokar hana zirga-zirga daga karfe bakwai na yamma zuwa bakwai na safe akan masu ababen hawa a jihar saboda rashin wadataccen tsaro amma rundunar yansanda bata ce komai ba akan maganar da ya yi.