Za a Taimakawa Mabukata 2,000 da Gabobin Roba A Kaduna.

181

Cibiyar agaji ta kasar Indiya mai suna Ishk Tolaram Limbs centre ta bada kyautan gabobin jikin dan Adam na roba ga mabukata a jihar Kaduna.

Shugaban sashen kere-kere da gudanarwa na cibiyan mista Jaiprakash Bidlan yace sun yanke shawarar bada kyautar gabobin jikin na roba ga mutanen Kaduna wanda basu da ikon siyawa kansu.

Shugaban ya kara da cewa, a yanzu haka suna da mutum 98 wanda zasu amfana da agajinsu amma suna da niyyar agazawa mutane dubu biyu ne kuma har zuwa yanzu suna daukan rijistar mabukata domin samun wannan adadin.

Baya ga haka, mista Bidlan yace ba su kadai suke wannan aiki ba, suna samun tallafi daga wasu kamfanoni, don haka gabobin na roba idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, zasu dade ana cin moriyarsu.

Ya kara da cewa, cibiyarsu ta dade tana taimakon mutane da suke fama da rashin gabobi a kasar, domin kuwa kididdiga ya nuna cewa mutum 15,000 ne suka amfana da aikinsu kuma zasu cigaba da yin wannan agaji a kasarnan.

Daga nan ya yi kira ga gwamnati da ta bada gudunmawa don samun karuwar masu cin gajiyar cibiyar.

Kwamishinan mata da cigaban al’umma ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta ce cibiyar ta zo jihar tun watan maris din shekarar nan domin daukar gwajin gabobin masu cin gajiyar shirin.

Ta kara da cewa, akwai kyakkyawar alaka tsakanin cibiyar da gwamna Nasiru El-Rufa’i wanda hakan yasa suke taimakawa yara da manya da suke bukatar gabobin jiki na roba kamar kafa da hannu da sauransu.

Daga karshe ta yi godiya ga cibiyar a madadin gwamnatin jihar Kaduna da kuma wanda suka ci gajiyar shirin bisa bada agajin kyauta a jihar ta Kaduna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan