Ali Nuhu da Adam A. Zango manyan jarumai ne a masana’antar Kannywood, sai dai kowa daga cikin yana da irin ra’ayinsa da kuma yadda yake gudanar da al’amuransa na yau da kullum, har wa yau sun sha samun sabani a tsakaninsu wanda hakan ya dinga shiga har cikin magoya bayansu.

Idan ba a manta ba a watannin da suka gabata ne jaruman biyu suka shirya idan aka dinga gani suna musayar kalamai na nuna zumunci da kuma yafiya ga juna. Amma a wannan karon a iya cewa ta sauya zani domin Adam A. Zango yayu amfani da shafinsa na Instagram inda na wallafa wani rubutu, kuma rubutun cike yake da zagi da cin mutunci kuma ya rubata ne kai tsaye zuwa ga Ali Nuhu wanda mutane da dama suke ganinsa a matsayin sarki na masana’antar Kannywood. Adam A. Zango ya wallafa rubutun ne a matsayin martani ga Ali Nuhu, wanda yake ikirarin cewa Ali Nuhu ne yasa yaransa suka zagi mahaifiyarsa shi yasa shi ma ya rama. Kuma yace yanzu ya fara maida martani daga abinda ake masa.