Kasar Saudiyya Ta Bada Agaji Ga Marayu 2,073 A Jihar Kebbi

159

Wata kungiya mai suna Saudi Arabia International Islamic Relief Organisation ta fara bada agaji na kudi ga marayu 2,073 a jihar Kebbi domin rage musu wahalhalun rayuwa.

Babban sakatarn kungiyar Dr Abdulaziz Al-sarhan ne ya bayyana haka a jiya lahadi, bakwai ga watan Afrilu a garin Birnin Kebbi.

Dr Abdulaziz ya ce marayun da zasu ci gajiyar agajin sun fito daga kananan hukumomin Birnin Kebbo, da Galumbe, da Gwandu, da Argungun, da Jega, da Koko, da Shanga, da Yauri.

Shugaban gudanarwa na kungiyar na jihar Kebbi, malam Tahiru Baba-Ibrahim ya ce za a raba kudaden agajin bisa yawan shekarun rijista da kungiyar, kuma bai bayyana yawan kudaden da za a raba ba saboda sha’anin tsaro.

Malam Tahiru wanda ya gudanar da jawabi a lokacin da ya ke kaddamar da shirin, ya ce wasu daga cikin marayun sunyi rihista shekaru uku da suka wuce yayin da wasu sunyi rijista shekaru biyu da suka wuce, don haka adadin kudin da za a basu ya bambanta.

A nasa bangaren, Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Bagudu ya bayyana wa kungiyar cewa, jihar Kebbi ta fi kowanni jiha yawan yan gudun hijirar fadan Boko Haram wanda suka fito daga jihohin Borno da Yobe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan