Martani: Kasar Saudiyya Ta Yi Magana Akan Kashe Yar Najeriya Da Ta Yi

345

Ofishin Jakadancin Masarautar Saudi Arabia da ke kasarnan sun mayar da martani akan batun kissan wata mata yar Najeriya da kasr ta yi bisa kamata da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Ambasada mai wakiltar Kasar Saudiyya a kasarnan, Adnan Bostaji ya bayyana haka a ma’aikatan harkokin kasashen na kasarnan da ke garin Abuja.

Adnan Bastoji ya ce duk mai zuwa kasar Saudiyya yana sane da hukuncin kisa da ta dora akan duk wandavaka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi. Don haka hukuncin da kasar ta yanke kan yar Najeriya Kudirat Afolabi, da maza Yan kasar Pakistan biyu da Dan Kasar Yemen yayi dai-dai.

Ambasadan ya kara da cewa, kasar Saudiyya tana amfani da dokokin shari’a a matsayin tsarin mulkin ta, kuma shari’ar Musulunci ya haramta safarar miyagun kwayoyi, shi yasa suke yin hukuncin da ya dace ga duk wanda ya karya dokan kasarsu, ko wanene idan har an kama mutum da laifi.

Ambasada Adnan yayi bayanin cewa ana bin wasu matakai daki-daki kafina a zartar da hukuncin kisa akan masu laifi kamar haka; Ana bawa masu laifi damar kare kansu a kotu, wanda basu da damar daukan lauya, gwamnati na basu shi kauta. Sannan suna tuntubar ofishin jakadancin kasar masu laifi domin sanar da su abinda yake faruwa domin bin kadi. Sai an tabbatar an gama bincike tsaf, tare da bayyana duka wata shaida da hujja, kuma an samu mutum da laifi, to a nan ne kasar saudiyya ke yanke hukuncin kisa.

Adnan Bastoji ya bayyana takaicinsa, inda ya ce duk da irin tsauraran matakan da kasar ta ke da shi akam miyagun kwayoyi, har yanzu ana samun bakin da ke shigowa da shi cikin kasar Saudiyya. Kafin a ba mutum izinin shoga kasar, sai ya sa hannu a takarda ta amincewa da dokar Miyagun Kwayoyi akan sa. Don haka zasu cigaba da kare kasarsu daga masu safarar miyagun kwayoyi walau baki ne ko yan kasa, doka zata yi aiki a kan kowa.

A nasa bangaren Ambasada mai wakiltar kasarnan a kasar Saudi Arabiya, Isa Dodo ya bayyana damuwarsa akan yadda yan Najeriya da sauran kasashe ke safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar.

Ya kara da cewa, dokar kasar Saudiyya kan masu safarar miyagun kwayoyi a bayyane ta ke kuma babu wanda ya isa ya hana gwamnati aiwatar da hukuncin. Don haka ya rage namu musan yadda zamu hana mutanen mu safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar da sauran kasashen duniya baki daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan