Takarar Shugaban Majalisar Dattijai: Sanata Ndume ya matsa ƙaimi

A yau ne Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wata ganawar sirri da Sanata Ali Ndume a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa, Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bada rahoton cewa Sanata Ndume ya isa Fadar Shugaban Ƙasar da misalin ƙarfe 3:20, kuma kai tsaye ya wuce zuwa Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Manema labarai dake Fadar ta Shugaban Ƙasa ba su san maƙasudin tattaunawar ba.

Amma NAN ya ce ganawar ba za ta rasa nasaba da zaɓen sabbin shugabannin da za su jagoranci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta 9 ba.

Shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa dai ya roƙi sabbin ‘yan Majalisun Dokoki da aka zaɓa da su mara wa ‘yan takarar da jam’iyyar ta zaɓa baya idan an zo zaɓen shugabannin Majalisar.

Jam’iyyar ta tsayar da Sanata Ahmed Lawal a matsayin ɗan takarar Shugaban Majalisar Dattijai, sai kuma Femi Gbajabiamila a matsayin ɗan takarar Kakakin Majalisar Wakilai.

Amma Sanata Ndume ya dage wajen ci gaba da yin takarar shugabancin Majalisar Dattijan.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan