Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kashe-kashe da ke afkuwa a jihar a tsawon shekara biyar.
Gwamnan jihar Alhaji Abdulaziz Yari ne ya bayyana hakan a lokacin da suke yin taron masu ruwa da tsaki tare da sufeto-janar na ‘yansanda Muhammad Adamu ranar Talatar da ta gabata.
Gwamnan yace an kashe kimanin mutane dubu 3,526 yayinda aka jiwa dubu 8,219 raunuka kuma an tarwatsa kauyuka kusan 500 a jihar.
Gwamnan, wanda sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Shinkafi ya wakilta yace sama da hekta dubu 13,000 aka lalata, hakan yasa manoma ba zasu iya amfana da su ba. Wannan dalili yasa tattalin arzikin jihar yake cikin wani yanayi domin kuwa maharan sun kone dubunnen shaguna, tare da koran mutane daga mazaunansu saboda tsoron abin da zai biyo baya.
Gwamnan yace gwamnatinsa ta rubuta cikakken rahoto mai shafi dubu 7,000 dauke da bayanai dalla-dalla akan faruwar lamarin kawo yanzu. Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta san sansanin ‘yan ta’addan guda takwas da suka shahara, boye a dazuka daban-daban a jihar. Don haka yake kira ga gwamnatin tarayya dasu magance lamarin ta hanyar kama ‘yan ta’addan.
Daga karshe, gwamna Yari yace kokarin gwamnati na dakatar da hakan ma’adinai sai an hada da aikin jami’an tsaro domin magance lamarin baki daya.