Gwamnatin Kasar Birtaniya ta yi wa dokokin saki garambawul a Ingila da Wales yanda ma’aurata zasu samu sauki da hanzari idan sun tashi rabuwa.
Sakataren shari’a na Birtaniya ne ya bayyana haka, biyo bayan hukuncin kotun kolin kasar na kin amincewa da bukatar wata mata da ta nemi kotun ta raba auren ta da mijin da suka kwashe shekaru 20 suna tare.
Mista Gauke ya ce sauyi a dokar sakin zai kawo karshen suka ko ďora laifi da ma’aurata kanyi wajen gabatar da dalilin neman saki.
A bisa tanadin dokojin da sukke da su a yanzu, idan daya daga cikin ma’aurata ya zargi dayan da aikata Zina ko kuma wata dabi’a maras kyau a matsayin dalilin saki, shari’a zata iya daukar wata uku zuwa shida kafin a tabbatar da rabuwa.
Amma idan sakin an neme shi bisa wasu dalilai ne na dabam, to rabuwa zai iya daukan lokaci mai tsawo kamar shekara biyu idan har ma’auratan duk sun amince a rabu. Ko kuma shekara biyar idan daya daga cikin ma’auratan ne ya amince da rabuwar.
Babbar mai shari’a ta kasar Birtaniya, Baroness Hale tana daya daga cikin masu neman a yiwa dokokin gyara wanda ta ce babu adalci a cikinsu.
Sabbin dokokin sun tanadi mafi karancin wa’adin na wata shida domin rabuwa daga lokacin da aka shigar da karar neman sakin auren. Bayan haka, a karshen wa’adin za a bukaci wanda ke son a raba auren da ya tabbatar da cewa yana kan bakansa kafin a bayar da damar sakin.
Gwamnati ta ce wa’adin na wata shida zai bawa mutum dama ya yi tunani akan rabuwar ko kuma ya canza shawara. Akan batun Matakin sabunta dokoki, gwamnati ta dauke hukuncin ne biyo bayan tuntubar da ta yiwa jama’a a tsawon sati biyu kuma sun nuna amincewarsu. Haka zalika ana sa ran garambawul din zai hana rikici tsakanin ma’aurata wanda yawanci yana bata rayuwar ýaýansu.