Ko ya ake ciki game da takarar Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya?

181

Labarin da BBC Hausa ta wallafa na cewa sabbin zaɓaɓbun ‘yan Majalisar Dokokin Najeriya sun ƙi yarda tare da jan daga da kuma fitowa takarar mukamin Kakakin Majalisar Wakilai, da za a kafa duk da cewa jam`iyyar APC mai mulki ta ce za ta keɓe muƙamin ga shiyya ɗaya kawai.

Wasu jiga-jigan jamiyyar dai na yin isharar da ke nuna cewa za a kebe mukamin Kakakin ne ga shiyyar kudu-maso-yammacin kasar, daga cikin shiyyoyi shida amma wasuyan majalisar na cewa ba za ta sabu ba.

BBC ta ci gaba da cewa ya zuwa yanzu dai wadanda suka fito takarar mukamin na shugaban majalisar wakilan Najeriyar sun zarta mutum goma, kuma kowanne ya ja daga da cewa shi ya fi cancanta.

Honorabul Muhammadu Umaru Bako daga shiyyar Arewa ta Tsakiya, wanda yake cikin masu takarar ya ce, yankinsu ne ya fi dacewa da muƙamin, idan aka yi la’akari da kason muƙaman da wasu shiyyoyin suka samu.

Ya ce: ”Wannan naman guda shida a kan tebur, an ɗauka ɗaya an ba Arewa Maso Yamma (muƙamin Shugaban Ƙasa), an ɗauka Mataimakin Shugaban Ƙasa an kai ma Kudu Maso Yamma, Senet an kai ma Arewa na Gabas.

Ya ake so a yi da mu? Ba za a iya tauye mana haƙƙi ba, gaskiyar magana ke nan.”

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa, ”Babu gudu ba ja da baya. Mu dai mun san cewa in za a yi mana adalci mu ne ya kamata, in ba a yi mana adalci kuma to shi ke nan adalci zai ba mu.”

A cewar BBC, tun a kwanakin baya jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ta yi wata ganawa da ‘yan Majalisar Dokokin da za su kafa majalisar dokokin kasar ta tara.

A lokacin ta bayyana cewa za ta fito da tsarin rarraba muƙaman majalisun a tsakanin shiyyoyin ƙasar cikin mako ɗaya, amma har yanzu ba ta fito da tsarin ba.

Da BBC ta tambayi Sakataren Walwala na Jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Masari, kan wannan magana sai ya ce, ba su kai ga zaman yanke wannan matsaya ba.

Sai dai yana ganin ƙila zuwa karshen makon da ake ciki Majalisar Zartarwa ta Jam’iyyar ta APC, za ta zauna domin fitar da wannan matsaya.

Dangane da matakin da jam’iyyar ke neman ɗauka na rarraba muƙaman har wasu ke ƙalubalantar hakan da cewa dole ne a bi tsarin dumokuraɗiyya, Alhaji Ibrahim ya ce hakan ba wata matsala ba ce da za ta iya kaiwa ga jam’iyyar ta yi asarar muƙaman, kamar a baya ba.

Ya ce, dukkanin sabbin ‘yan majalisar sun yarda cewa jam’iyya ce take da da nama, kuma duk mai yi mata biyayya wajibi ne ya amince da matsayin da za ta fito da shi.

Yayin da ake ta wannan ce-ce-ku-ce da rububi kan neman muƙamin Kakakin Majalisar Wakilan ta Najeriya, har yanzu jam’iyyar ta APC ba ta iya shawo kan ‘ya’yanta ba da suke ja da matakinta na keɓe mukamin Shugaban Majalisar Dattawa ga shiyyar Arewa Maso Gabashin Ƙasar ba, har ma kuma da ayyana wanda take son ya samu muƙamin.

Wasu masu lura da al’amura dai na ganin idan jam’iyyar ba ta yi taka tsan-tsan ba, wadannan matsaloli za su iya jefa ta cikin ruɗani, har ma ta yi asarar muƙaman.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan