Shugaba Buhari Ya Yanke Ziyararsa Saboda Rashin Tsaro A Kasarnan

257

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke ziyararsa inda ya dawo gida Najeriya a daren jiya Talata , 9 ga watan Afrilu biyo bayan kashe-kashe da hare-hare da ya auku a jihohin Zamfara da Kaduna da sauran al’amuran kasa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewa ana sa ran shugaba Buhari zai dawo ne a yau Laraba amma sai jirgin sa ya sauka a Nnamdi Azikiwe airport dake garin Abuja a karfe 10:45 na daren jiya.

Kamfanin na NAN ya jiyo daga majiya mmai tushe cewa shugaban ya yanke hukuncin dawowa ne biyu bayan matsalolin tsaro da ke afkuwa a kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Kasarnan a ranar 4 ga watan Afrilu zuwa garin Amman domin amsa gayyatar sarki Abdallah na Kasar Jordan don hallartar taron tattalin arziki na duniya (World Economic Forum).

Daga nan shugaban Kasa Buhari ya zarce taron hadaddiyar Daular Larabawa na shekara-shekara na sanya hannun jari da aka yi a kasar Dubai. A yayin ziyarar, shugaban kasar ya gudanar da jawabai da kuma tarurruka da mutane da kungiyoyi da dama akan saka hannun jari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan