Tura Ta Kai Bango: Jama’a Yan Sa Kai Sun kashe Masu Satar Mutane 40 A Jihar Katsina

85

Wasu mutane da ke zaune a yankunan kananan hukumomin da ke makwabtaka da dajib Kamako sunyi gangamin sa kai inda suka hadu a garin Dungun Ma’azu da ke yankin karamar Hukumar sabuwa a jihar Katsina kuma suka shiga dajin don kaiwa maharan da ke addabarsu samame.

Wani Ganau da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa BBC Hausa cewa akalla mutane sama da 500 ne suka hallara a gangamin daga yankunan karamar Hukumar Katsina da na Jiar Kaduna domin shiga wannan dajin. Dajin Kamako babban daji ne da yayi iyaka da Birnin Gwari, da Zamfara, da Jihar Niger.
Ganau din ya kara da cewa anyi karan batta sosai a tsakanin yan sa kan da masu satar mutane kuma akalla an kashe masu satar mutane 40 yayin da aka kashe masu Sa kai mutum 21.

Ya kara da cewa, samamen ya yi matukar tasiri domin kuwa da komawarsu washe gari sai suka tarar babu kowa a wurin, duk sun gudu

Mutumin ya yi bayanin cewa sun dauki wannan mataku domin kawo karshen satar mutane da ake yi don kudin fansa a yankunan su, da hare-haren da ake kaiwa cikin kauyuka babu gaira babu dalili. Don gudun kar abun ya ta’azzara ya hana su noma ganin hukumomi ba su dauki wani mataki ba.

A nasu bangaren, BBC Hausa ta tattauna da mai magana da yawun rundunar Yansandar Jihar Katsina SP Gambo Musa wanda ya bayyana abun da jama’ar suka yi a matsayin sabon salo na yin gaban kansu.

SP Gambo ya ce yan Sa Kan ba daya suke da kungiyar Sintiri baa kuma ba su da goyon bayan hukuma. Daga nan ya gargadi jama’a da su guji aikata irin haka saboda hatsarin da ke ciki.

Ya kara da cewa Rundunarsu da hadin kan sojoji na iya bakin kokarinsu domin shawo kan matsalolin satar mutane da kuma kisa babu dalili a kauyukan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan