Yadda za ka zama kamar ni- Dangote

106

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote ya bai wa matasan nahiyar shawarwari idan suna son zama kamarsa, kamar yadda BBC Hausa ta bayyana.

Hamshaƙin attajirin ya bayyana hakan ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da attajirin nan ɗan ƙasar Sudan, Mo Ibrahim a birnin Abidjan na ƙasar Kwaddibuwa ƙarshen makon jiya.

Wani mahalarcin taron ya tambayi attajirin waɗanne ɓangarori zai fi mayar da hankali idan a ce yana a matsayin ɗan shekara 21 da haihuwa kuma yana shirin fara kasuwanci.

Dangote ya ce zai fi mayar da hankali ne a harkarkokin sadarwa na zamani da kuma aikin gona.

“Waɗannan ne bangarori biyu da za su fi kawo riba,” in ji shi.

Sai dai daga nan ya ja kunnen matasa game da ɗabi’unsu bayan fara kasuwanci musamman ‘yan Afirka.

Ya ce muna “kashe ribar da ba ta kai ga zuwa hannunmu ba.”

“Da zarar ka fara kasuwanci kuma kasuwancin ya fara samun ci gaba, maimakon ka yi ta ƙara uwar kuɗin, sai mutum ya fara kashe kuɗin da tunanin ribar za ta ci gaba da zuwa,” kamar yadda ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa: “Dole ne mutum ya natsu saboda akwai ƙalubale nan da can.”

Attajirin ya ce bai kamata mutum ya fara kashe kuɗi ba ba-ji-ba-gani ba.

“Saboda idan ka sayi manyan abubuwan more rayuwa (kamar motocin ƙawa) za su ɗauke maka hankali daga harkokin kasuwancinka.”

Daga nan, ya bayar da misali da kansa, inda ya ce “ba ni da wani gidan shaƙatawa mallakina a ko ina a faɗin duniya.”

“Amma akwai wasu daga cikin ma’aikatana da suke da gidan shaƙatawa a birnin Landan.”

‘Na taba ciro $10m lakadan daga banki’


Dangote ya bayyana cewa ya taɓa zuwa banki inda ya karɓo Dala Miliyan 10 domin ya tabbatar da cewa da gaske yana da kuɗi.

Dangote ya bayyana cewa da ya je bankin, ya rubuta takardar karɓar kuɗi sai ya karɓi kuɗin lakadan sa’annan ya zuba su a bayan motarsa.

Sai dai ba kashe kuɗin ya yi ba, “washegari na mayar da su banki domin ci gaba da ajiyarsu,” in ji shi.

Da aka tambaye shi nawa yake da shi a cikin aljihunsa a lokacin hirar, sai ya ce “za ka yi mamaki. Babu ko sisi a aljihuna, ko dala ɗaya babu a ciki.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan