Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar katsina ya nuna damuwarsa bisa yadda yan Ta’adda ke damun jihar ta Katsina.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya laraba 10 ga watan Afrilu a lokacin da ya ke ganawa da Mukaddashin sufeto janar na Yansanda Muhammad Adamu a jihar.
Gwamnan wanda ya samu wakikcin mataimakinsa Mannir Yakubu ya ce gwamnatinsa ta gana da shugabannin kananan hukumomi takwas da abun ya shafa domin samun bayanai saboda gwamnati ta yi niyyar daukan dukkan matakin da zai kawo karshen aikin yan ta’addan.
Gwamnan ya kara da cewa sufeto Janar din yazo a dai-dai lokacin da ake cikin zulumi kuma jihar katsina zata bada goyon baya da gudumawa na kudi, da wurin zama, da kayan aiki ga shirin rundunar Yansanda na ‘Operetion Puff Adder’. A wurin ya sanar da kyautar motoci guda 12 kirar ‘Van’ da gwamnati ta bayar ga rundunar.
Daga nan ya yi bayani cewa masu garkuwa da mutane da yan ta’adda sun kai hari wasu sashen jihar tare da lalata dikiya da gidajen al’umma. Abun bai tsaya nan ba, har gidaje suke bi suna sace mutane kamar yadda suka dauke surukar gwamna a gidanta. Kananan hukumomin da abin ya shafa su ne Batsari, da Dandume, da Dan-Musa, da Faskari, da Jibiya, da Kankara, da Sabuwa, Da Safana.