A ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Kano ta garƙame wani shahararren otel, mai suna Mbanefo Holiday Inn dake kan titin Abeokuta dake yankin Sabon Gari a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN, ya bada rahoton cewa lokacin da aka kulle otel ɗin, ma’aikatan da suka yi aikin rufe hotel ɗin sun kama mutane 28 waɗanda suka haɗa da mata masu zaman kansu 19 da wasu mutum uku ‘yan ƙasashen waje dake zaune ba bisa ƙa’ida ba.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kaɗan bayan rufe otel ɗin, Manajan Daraktan Hukumar Kula da Yawan Buɗe Ido ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Mu’azu Gwarzo ya ce an rufe otel ɗin ne sakamakon keta dokokin da ke tafiyar da aikace-aikacen otel-otel a jihar.
Ya ce kimanin wata bakwai da suka gabata, Hukumar Kula da Shige da Fice, NIS a jihar ta kama baƙi ‘yan ƙasashen waje dake zaune ba bisa ƙa’ida ba har 14, waɗanda suka haɗa da ‘yan Cadi da ‘yan Kamaru.
“Muna aiki ne bisa umurnin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda abubuwan da suka saɓa doka da ake yi a otel ɗin.
“Kimanin kwanaki tara da suka gabata, mun gayyaci masu otel ɗin sakamakon wasu abubuwa da suka saɓa doka. Idan muka ƙyale waɗannan abubuwa suka ci gaba, Allah ne kaɗai Ya san me zai faru a otel ɗin”, in ji Mista Gwarzo.
Ya ce ana zargin masu otel ɗin da shigo da waɗanda ba ‘yan Najeriya ba, ‘yan mata masu ƙananan shekaru da sauran masu aikata laifi.
Bugu da ƙari, ya ce masu hotel ɗin sun mayar da hotel ɗin kamar gidan karuwai inda ake yin amfani da ɗakunan na ‘taƙaitaccen lokaci’, wadda hakan ƙarara ya saɓa wa dokokin dake tafiyar da aikace-aikacen otel-otel a jihar.
Mista Gwarzo ya gargaɗi masu otel-otel a jihar da su yi biyayya sau da ƙafa ga dokokin dake tafiyar da aikace-aikacen otel-otel a jihar, saboda Gwamnatin Jihar ba za ta yi wata-wata ba wajen garƙame duk wani otel ta samu yana karya dokokin.
Ya ce Gwamnatin Jihar za ta ci gaba da lura da yadda otel-otel ke tafiyar da aikace-aikacensu a jihar don tabbatar da tsafta a ciki.
Da yake magana da manema labarai tun da farko, Manajan Otel ɗin, Bonnyface Anayachukwu ya ce: “Na yi wa otel ɗin rijista, amma daga baya aka ƙwace lasisin, kuma aka buƙace ni da in sake sabo.
“Shekara 40 kenan muna aiki, idan ba mu da rijista, ya za a yi mu yi aiki tsawon waɗannan shekaru?”.
Amma ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta sake buɗe otel ɗin, saboda a cewarsa, a shirye yake ya bi dokokin dake tafiyar da aikace-aikacen otel-otel a jihar.
Wasu daga cikin matan da aka kama sun ce sun zo ne daga jihohin Kaduna, Borno da Nasarawa.
An mika waɗanda aka kama ɗin su 28 zuwa Ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice na Jihar don tantancewa.