Ko kun san yadda aka yi sojoji suka hamɓare Omar al-Bashir?

166

Bayan shekaru 30 kan karagar mulki, Sojoji sun hambarar da gwamnatin Shugaban Sudan, Omar al-Bashir kamar yadda ministan tsaro na kasar ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan doguwar zanga-zanga da kuma matsin lamba da shugaban ya samu daga ‘yan kasar, kamar yadda BBC ta wallafa.

BBC ta ci gaba da cewa:


Sojoji sun hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir.


An tura sojoji kan titunan Khartourm, babban birnin ƙasar Sudan.


Ana cece-kucen wata kila a yau al-Bashir ya miƙa mulki.

Al-Bashir ya yi kusan shekara 30 a kan mulki.


An yi kwana shida a jere ana zanga-zangar adawa da al-Bashir.


Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) tana nemansa ruwa-a-jallo.

Rahoton na BBC ya ci gaba da cewa:


Wannan wani juyin mulki ne da babu cikakken bayani kan yadda manyan sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Sudan za su miƙa mulki ga farar hula.

Jami’an tsaro a ƙasar tuni suka lissafa cewa hambarar da al-Bashir da kuma saka dokar hana fita zai samar masu lokaci kuma a kawo ƙarshen zanga-zangar.

Idan wannan maganar haka ne, akwai rashin lissafi a wannan lamari domin kuwa ƙungiyar da ke jagorantar zanga-zanga a Sudan wato Sudanese Professionals Association da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu tuni suka bayyana cewa ba za su yadda da wannan jawabin da Shugaban Sojojin Ƙasar ya yi ba.

Ƙungiyoyin suna da ɗumbin magoya baya kuma a shirye suke, haka kuma su ma sojoji a ƙasar suna da bindigogi da kuma karfin take duk wanda ya tayar da tarzoma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan