Rikicin Zamfara: Gwamnatin Tarayya Na Zargin Wasu Yan Jihar Da Hannu

229

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa akwai hannun manyan jihar Zamfara a cikin matsalar kashe-kashe da ya addabi jihar.

Ministan Tsaron Kasa Mansur Dan Ali ne ya bayyana haka a wani sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Col. Tukur Gusau a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu.

Gwamnatin tarayya tana zargin akwai sa hannun sarakunan gargajiya da ke taimakawa yan ta’addan su gudanar da miyagun aiyuka a jihar. A satin da ya gabata ne aka kashe sama da mutum 50 a jihar kuma hakan ya janyo Allah wadai da kalaman suka ga gwamnatin bisa sakacin ta akan lamarin ganin yawan mutanen da ake kashewa.

Dan haka, ministan ya ja kunnen wani mutum ko kungiyar mutane da suek hada baki da yan ta’addan wajen aikata laifuka da su tuba ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Ya kara da cewa an bawa rundunar sojojin kasar nan umarnin yin hukunci mai tsauri ga duk wanda aka kama da hannun wajen taimakwa yan ta’addan, ko wanene kuma komai mukaminsa.

A bangare guda babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana takaicin ta bisa kashe-kashe da ke faruwa a jihar. Ta kuma zargi gwamnati da nuna halin ko in kula akan lamarin ta bakin sakataren yaďa labaranta Kola Ologbondiyan.

PDP ta yi kira ga jam’iyya mai mulki na APC da tazo ta yi bayani akan yan daban siyasa da ta yi hayan su daga kasashen Chadi da Nijar domin magudin zaben kasa na shekarar 2019.

Jam’iyyar PDP ta yi kiran ne bisa tsoron tabbatar hasashen da ya ke yi na yiwur wadannan yan dabar siyasan da APC ta dauko ke da hannu a matsalolin tsaro a wasu jihohin kasarnan.

Daga karshe PDP ta bayyana takaicinta ganin yadda gwamnatin tarayya ta gaza kare rayukan yan kasa da kawo katshen garkuwa da mutane, da zubda jini a jihohin Adamawa, da Bauchi, da Borno, da Kaduna, da Kogi, da Plateau, da Taraba, da Zamfara da kuma sauran jihohin Kasarnan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan