Turkashi! Yan Najeriya 446 Ke Zaman Gidan Yari A Gabas Ta Tsakiya

183

Ambasada mai wakiltar kasarnan a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Muhammad Rimi ya ce kimanin yan Najeriya 446 ke zaman gidan kasi a gidajen yari dabam-dabam a gabas ta tsakiya.

Ambasada Rimi ya bayyana haka a lokacin da suka yi taron masu ruwa da tsaki da shugaban kasa Muhammad Buhari da Yan Najwriya a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya ce yan Najeriyan 446 an kama su ne bisa laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi da aikata fashi da makami. Duk da haka gwamnatin UAE ta yi afuwa ga yan Najeriya masu laifi su dubu 5000.

Muhammad Rimi ya kara da cewa gwamnatin UAE tana bada goyon baya ga Yan Najeriya da son rauywa a can don gudanar da kasuwanci ko wasu halastattun aiyuka.

Yanzu haka, sama da yan Najeriya dubu 10,000 ke rayuwa a can kuma daga ciki akwai dalibai 2,017. A shekarar 2018 kawai, gwamnatin UAE ta bada izinin shiga kasar ga yan Najeriya 5,774.

A nashi bangaren, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa zata maida hankali akan karfafa aiyukan da suka yi a wa’adinsu na farko tare da cika alkawarurrukan da ya yi a lokacin yakin neman zabe musamman harkar Tsaro, da Tattalin Arziki, da Kuma Yaki da Cin hanci da rashawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan